--
Ana ce-ce-ku-ce kan batun ministan na maye gurbin lambar BVN da NIN Duba Abinda ake cewa

Ana ce-ce-ku-ce kan batun ministan na maye gurbin lambar BVN da NIN Duba Abinda ake cewa


Ƴan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabambanta game da kalaman ministan sandarwar ƙasar Isa Ali Fantami, na cewa akwai yiwuwar maye gurbin lambar tattara bayanan banki ta BVN da lambar katin ɗan ƙasa ta NIN.

Ministan ya yi batun ne yayin zantawa da ƴan jarida yayin wata ziyarar shaida yadda aikin mallakar katin ɗan kasa ta NIN ke gudana a Abuja.

A cewarsa ''lambar tattara bayanai ta BVN masu asusun ajiya a banki ne kawai ke da damar mallakarta, ba kamar lambar katin ɗan ƙasa ba ta NIN da duk wani ɗan Najeriya ke da haƙƙi da ita.''

Isa Ali Pantami ya ƙara da cewa irin matakan da ƙasar ke dauka tun kafin aje ko ina ''ta shiga gaban dukkan ƙasashen Afrika idan ana maganar tsare bayanan ƴan ƙasa.''

To sai dai kalaman ministan sun ta da ƙura a ƙasar musamman a shafukan sada zumunta, inda ƴan ƙasar ke bayyana ra'ayoyi mabambanta kan furucin.

Yayin da wasu ke ganin abu ne mai kyau kasancewar ba kowane ɗan Najeriya ne ke da damar mallakar lambar BVN ba, wasu kuma na ganin idan haka ne tun da farko babu buƙatar a wahalar da al'umma da cewa su mallaki lambar BVN tun da suna da ta NIN.

Wani ɓangare kuma a maimakon yabo ko suka, shawarwari suka bayar kan yadda za a sauƙaƙa aikin, tare da ɗaukar matakan kare kuɗaɗen al'umma daga masu satar bayanai ko kuɗaɗe a intanet.


Abin da mutane ke cewa a Tuwita:



@ImohUmoren ya ce: "Suna son maye gurbin BVN da NIN? Muna jira mu ga nan gaba abin da wani ministan ko a wace ma'aikata ce zai zo da shi don maye gurbin NIN @ChinaksChris_ ya ce: "An samar da lambar BVN ne don gano mutane masu cin hanci, yanzu kuma gwamnati tana son sauya shi da NIN. Anya cin hanci ake yaƙa kuwa?" Shi kuwa @MFaarees_ cewa ya yi: "Ƙoƙarin Pantami na maye gurbn BVN da NIN abu ne mai kyau gaskiya, BVN aikinsa ha harkar kuɗaɗe na banki ya tsaya kawai, amma NIN za ta iya aiki a kowane fanni na hada-hadar duniya, kuma ta fi zama abin dogaro. Ina ga ko katin zaɓen ma za a iya maye gurbinsa da NIN. Bayanan da ke kan lan]mbar katin zama ɗan ƙasa su ne kawai abin da ake buƙata a duk ƙasashen da suka ci gaba." @HinduMustafa ta ce: "@DrIsaPantami idan kana son maye gurbin BVN da NIN, me zai hana a mayar da lambar BVN da muke da ita yanzu zuwa NIN sai a umarci waɗanda ba su da ita su je su yi nasu. BVN tana da bayanan mutum da zanen yatsu da hoto. Ina ga hakan zai fi sauƙaƙ wa gwamnati da ƴan ƙasa. Short presentational grey line Yanzu haka ana kan ci gaba da haɗa layukan waya da lambar ɗan ƙasa ta NIN kamar yadda hukumomi suka umurta. A ɗaya ɓangaren kuma waɗanda ba su da lambar NIN na tururwa don yin rajistar kafin wa'adin da ma'aikatar sadarwa ta bayar ya cika.


MAJIYA: BBC HAUSA

Kukaranta sabbin labarai anan 

https://www.bzglobalservice.com.ng/

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook: 

https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter:

https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com


0 Response to "Ana ce-ce-ku-ce kan batun ministan na maye gurbin lambar BVN da NIN Duba Abinda ake cewa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?