An tsare akalla mutane 200 a Kano, 25 sun tafi gidan gyara hali duba dalili
Rahotanni sun nuna cewa kotun da ke hukunta wadanda suka karya dokar korona a jihar Kano, ta tura mutane 25 gidan gyara hali bayan ta kama su da laifi.
An tattaro cewa akalla mutane 200 jami’an tsaro suka tsare sakamakon karya dokar korona da gwamnatin jihar ta shimfida wanda daga cikinsu aka ci tarar wasu.
Shugaban hukumar Karota, Baffa Babba DanAgundi, ya ce: “Mun gode Allah da mutanen Kano ke bin dokar sanya takunkumin fuska domin kare lafiyarsu.
“Duk marasa bin doka da ke kin sanya takunkumin fuska za su hadu da fushin hukuma. Saboda haka dokar kariyar korona ta zauna ke nan.”
Bayan fara aiki da dokar sanya takunkumi, Gwamnatin Kano ta kafa kotun tafi-da-gidanka kimanin guda 21, wanda DanAgundi ke jagoranta.
Ya bayyan cewa an kama masu karya dokar har mutane 102 da aka ci tarar kowanensu N5,000. Ya kara jan hankalin shugabanin kasuwanni da tabbatar da bin dokar kare kai daga annobar.
Da yake jawabi, Kwamishinan Yada Labaran jihar, Muhammad Garba ya ce sabuwar dokar za ta tabbatar da kare mutane daga kamuwa da cutar korona.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne saboda yadda cutar ke kara yaduwa a jihar tun bayan sake bullarta a karo na biyu, jaridar Aminiya ta ruwaito.
Ya ce duk wanda kotun tafi-da-gidanka ta samu ya karya dokar to za a hukunta shi yadda doka ta tanada don haka ya ja hankalin jama’ar jihar da su kasance masu bin doka a kodayaushe.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "An tsare akalla mutane 200 a Kano, 25 sun tafi gidan gyara hali duba dalili"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?