--
An kama matashi da ya shirya tsafi don mayar da abokinsa kudi

An kama matashi da ya shirya tsafi don mayar da abokinsa kudi


Asirin wani matashi mai suna Oghenemara ya tonu lokacin da ya kammala shiri tsaf domin ya mayar da abokin zamansa a daki daya domin ya zama kudi.


Lamarin ga faru ne a gidan da yake zaune tare da abokinsa a Alvino hostel, staff quarter da ke garin  otefe Oghara, a jihar Delta.


Wanda aka kama ya kewaye dakinsa da Kendur (candles) kuma ya samo manyan jakka guda biyu tare da sauran ababen tsafi da suka wajaba domin yin tsafin.


Sai dai daga bisani Allah ya tona asirinsa, kuma makwabta suka kama shi suka yi masa dan banzan duka.


DAGA ISYAKU.COM

0 Response to "An kama matashi da ya shirya tsafi don mayar da abokinsa kudi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?