An ji karan tashin wani abin fashewa a jihar Kano, Duba abinda gwamnati ta ce anan
Monday, 15 February 2021
Comment
Jama'an gari sun ji karan tashin wani fashewa a jihar Kano. Wannan abu ya faru ne a unguwar Badawa Layout. Hadimin gwamnan Kano na yada labarai, Salihu Tanko Yakassai, ya bayyana cewa jami'an DSS sun dira wajen kuma babu wani abin tashin hankali.
A cewarsa, tukunyar Gas ce ta fashe a cikin wani gida. "Muna sanar da daukacin jama'ar Kano cewa tashin abin fashewar da akace ya faru a Badawa Layout sakamakon fashewar tukunyar gas ce, ba wani barazana bane na tsaro,"
Yakassai yace. "Jami'an tsaro na musamman DSS na wajen kuma babu wani abin tashin hankali."
Source: Legit.ng
0 Response to "An ji karan tashin wani abin fashewa a jihar Kano, Duba abinda gwamnati ta ce anan"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?