--
An bankado gidan ajiyar tabar wiwi, tare da kama mota makare da miyagun kwayoyi a jihar kudu kalli hotuna

An bankado gidan ajiyar tabar wiwi, tare da kama mota makare da miyagun kwayoyi a jihar kudu kalli hotuna


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), ta gano wata ma'ajiya ta tabar wiwi a yankin karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito. Mai magana da yawun hukumar, Jonah Achema, ya fadi haka a ranar Asabar a Abuja cewa hukumar ta kuma kama wata babbar motar daukar muggan kwayoyi a jihar. 


Da take bayar da bayani game da miyagun kwayoyi da aka kama a Benue, ga Shugaban Hukumar, Brig-Gen. Mohamed Buba Marwa, kwamandan hukumar ta NDLEA, Misis Florence Ezeonye, ​​ta ce adadin buhunan wiwi da aka kama a yayin kamen ya kai kilogram 1,578. 


A cewar ta: “Jami’an hukumar ta NDLEA reshen jihar Benue a cikin Makurdi, ta cake wata tirela da bata dauke da komai daga Awka, jihar Anambra da ke kan hanyarta ta zuwa Lafia, jihar Nasarawa. "Amma lokacin da aka bincika ta yadda ya kamata, an gano bulo 600 na tabar wiwi mai nauyin 600kg a wani daki da aka gina a karkashin motar.” in ji Ezeonye. A cewar ta, yanayin ɓoyewar shine irin sa na farko. 



Ta kara da cewa: “An sake yin kamun ne yayin da mutanenmu suka afka wa wani sito cike da kwayoyi da wasu manoma suka girba a yankin karamar hukumar Guma da karfe 3 na safe. “Adadin haramtattun magunguna da aka kwashe daga dakin ajiyar ya kai kilogram 978. "Dillalan miyagun kwayoyi sun harbe mutane na yayin da suka gansu amma an dakile harin nasu kuma a saboda haka, ba mu samu wani rauni ba." 


Kukaranta sabbin labarai anan 

https://www.bzglobalservice.com.ng/

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "An bankado gidan ajiyar tabar wiwi, tare da kama mota makare da miyagun kwayoyi a jihar kudu kalli hotuna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?