AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara : "Daukar Mataki Da Mu Ka Yi Yanzu Mu Ka Fara," In Ji Gwamna Ganduje
|
Daga cikin malaman da su ka tofa albarkacin bakinsu, sun hada da dan uwan AbdulJabbar din na jini, wato Alkali Mustapha Sheikh Nasiru Kabara, wanda ya bayar da shawarar cewar "Wannan magana ba wai magana ce ta muqabala ba. Wato ba maganar wai sai an zauna da shi ba ne. Ba abinda ya dace da shi illa a kai shi Kotun Musulunci."
Shi ma Limamin Masallacin Al-Furqan, Dr Bashir Aliyu Umar, cewa ya yi "Wannan ai ko kadan ba magana ce ta a zauna da wannan mutumin a yi Muqabala ba ne. Ai a irin wannan mas'ala a Musulunci ba a bukatar wai a ji dalilan mutum na yin abinda ya yi."
Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, shugaban Izalatul Bid'ah Wa'ikamatussunnah na Kano, kuma Shugaban Hukumar Alhazai Ta Jihar Kano, cewa ya yi "Ba maganar wata mahawara da wanda ya zagi Annabin Tsira Sallallahu Alaihi Wasallam."
Shi ma Shehi Shehi Maihula da Sayyadi Bashir Sheikh Tijjani Usman Zangon Barebari da Malamai da su ka yi magana a wajen, dukkansu sun hadu kan cewa ba bukatar zaman yin mahawara da duk mutumin da ya yi irin wadancan maganganu na batunci.
Sa'annan a jawabinsa na bude taro da takaitaccen bayani, Kwamishinan Harkokin Addini, Dr Muhammad Tahar Adam, ya bayyana irin sakonnin da su ke samu daga jama'a daban daban na yabawa da wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka.
Ya ce "Maigirma Gwamna, mu na ta samun sakonni daga gungun al'umma daban daban na goyon bayan wannan mataki da a ka fara dauka. Daga baya bayan nan mun samu sakon gaisuwa da jinjina daga Sarkin Musulmi da kuma Wazirin Katsina."
Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Alhamis, 4 ha Watan Fabrairu, 2021
cps@kanostate.gov.ng
fatimanbaba1@gmail.com
Hoto daga facebook Salihu Tanko Yakasai |
Majiya: facebook Salihu Tanko Yakasai
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:
https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter:
https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to "AbdulJabbar Sheikh Nasiru Kabara : "Daukar Mataki Da Mu Ka Yi Yanzu Mu Ka Fara," In Ji Gwamna Ganduje"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?