A karshe Buhari ya yi magana da babbar murya gameda kashe kashen da akeyi duba matakin da yace zai dauka
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari cewa ba zai bari wata kungiyar addini ko kabila ta jawo fada da rikicin kiyayya da juna a Najeriya ba.
Shugaban kasar ya fitar da jawabi ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, a ranar Lahadi, 14 ga watan Fubrairu, 2020 ta shafin Twitter.
Fadar shugaban kasar ta fito ta yi tir da rikicin da wasu bangare na kasar su ke neman su tada a Najeriya.
Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da abubuwan da ke faru wa a kudancin Najeriya inda ake hallaka mutanen wasu kabila, a garin Shashsa, jihar Oyo.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashi gwamnatinsa za ta kare dukkan kabilu da addinai; masu rinjaye ko marasa rinjaye, kamar yadda tsarin mulki ya daura mata nauyi.” Jawabin ya cigaba:
Shugaban kasa ya na gargadi cewa gwamnatinsa ba za ta bari wasu kungiyoyin addinai ko kabilu su tado da rikici da ta’adi a kan sauran jama’a ba.”
A jawabin da ya fitar jiya da daddare, Mai girma shugaban kasar ya tabbatar da cewa zai kawo karshen wannan kashe-kashe domin ganin abin bai yadu zuwa sauran wurare ba.
“(Buhari) ya yi kira ga shugabannin addini da gargajiya, har da gwamnoni da zababbun shugabanni a kasar, su hada kai da gwamnatin tarayya na ganin an samu zaman lafiya.”
Hakan na zuwa ne bayan kashe-kashen da aka yi sun jawo rashin rayukar Hausawa da dukiyoyinsu a Oyo.
Kukaranta sabbin labarai anan
https://www.bzglobalservice.com.ng/
Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24
Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:
bzglobalservicelabari@gmail.com
0 Response to " A karshe Buhari ya yi magana da babbar murya gameda kashe kashen da akeyi duba matakin da yace zai dauka "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?