--
‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargi da satar mota a Nasarawa, sun kwato master key a hannunsa

‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargi da satar mota a Nasarawa, sun kwato master key a hannunsa


Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Nasarawa ta cafke wani da ake zargi da satar mota tare da kwato wasu makullan masters daga wurinsa.


Kakakin rundunar, ASP Ramhan Nansel, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce wanda ake zargin, Adamu Yusuf, mazaunin Ungwan Osama, Masaka a karamar hukumar Karu, jami’an ‘yan sanda sun kama shi a ranar Litinin, 25 ga watan Janairu yayin da yake kokarin don satar mota.


kamar yanda shafin linda Inkeji ya wallafa "Jami'an 'yan sanda masu ido-da ido na Eagle-eyed da ke New Nyanya a karkashin gada sun kama wanda ake zargin a yayin da ya bude mota daya kuma yana shirin sata. Wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ana ci gaba da bincike bayan haka za a gurfanar da shi a gaban Kotu, "in ji ASP Nansel.


KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24

0 Response to "‘Yan sanda sun cafke wanda ake zargi da satar mota a Nasarawa, sun kwato master key a hannunsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?