Wata sabuwa: An fara yiwa mutane gwajin Korona ta hanyar tura auduga cikin duburansu
Gwamnatin kasar Sin ta fara yiwa mazauna Beijing gwajin Korona ta dubura Ana bukatar tura auduga cikin duburan mutum na tsawon inci daya Za'a juya audugar ciki akalla sau biyu cikin dakikai 10 sannan a cire
Masana sun bayyana cewa gwaji ta wannan hanyan ya fi bada sakamako na kwarai Kasar Sin ta fara yiwa al'ummarta gwajin cutar Korona ta hanyar tura auduga cikin dubura, wannan wata hanya ce da masana sukace tafi bada sakamako na kwarai, Daily Mail ta ruwaito.
Domin yin wannan gwaji, ana bukatar tura audugar cikin dubura na tsawon inci daya zuwa biyu kuma a juyashi. Bayan yin haka sau biyu, za'a cire audugar sannan ayi gwaji. Mahukunta a birnin Beijing sun fara wannan gwajin ne bayan kamuwar da wani yaro dan shekara 9 yayi da cutar Korona makon da ya gabata.
Wani masani a asibitin You'an dake Beijing, Li Tongzeng, yayin hira da tashar CCTV ranar Asabar, yace an gano kwayoyin cutar Korona sun fi dadewa cikiin dubura fiye da baki da hanci. "Mun samu cewa wasu masu cutar Korona da basu nuna alamu suna warkewa da wuri.
Akwai yiwuwan ba za'a samu cutar a makogwaronsu ba cikin kwanaki uku zuwa biyar," Li ya bayyana. "Amma cutar ta fi dadewa a samfurin da aka dauka na ba hayan mutum, idan aka hada da wadanda aka dauka daga wuraren irinsu baki, hanci da makogwaro."
MAJIYA LEGIT
KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:
FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24
0 Response to "Wata sabuwa: An fara yiwa mutane gwajin Korona ta hanyar tura auduga cikin duburansu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?