
Uwa da 'ya'yanta biyu sun kone kurmus a Bauchi Duba dalili
Wata uwa da ‘ya’yanta biyu sun kone kurmus a wata gobara da ta tashi a ƙauyen Riban Garmu, Unguwar Dewu da ke cikin Karamar Hukumar Kirfi a Jihar Bauchi.
Wasu mutane hudu sun samu raunuka a gobarar da ta lalata gidan mai dakuna hudu kuma a yanzu haka suna karbar kulawa a Babban Asibitin Kirfi.
Shafin LindaInkeji Ya Wallafa, An tattaro cewa gobarar ta afku ne sakamakon tartsatsin wutar da ke gidan yayin da dangin ke bacci.
A cewar wani ganau, uwar da ‘ya’yan nata suna ta kururuwar kuka suna neman taimako amma duk kokarin da aka yi na tilasta kofar gidan a bude domin kubutar da su ya ci tura.
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Kirfi a majalisar dokokin jihar, Hon. Abdulkadir Umar Dewu, ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan mamatan a madadin Gwamnan Jihar, Bala Mohammed. Ya gabatar da kyautar kudi N250,000 ga dangin a madadin Gwamna.
0 Response to "Uwa da 'ya'yanta biyu sun kone kurmus a Bauchi Duba dalili"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?