--
Tsohon Ministan Kasuwanci da Masana'antu, Jubril Martins-Kuye, ya mutu yana da shekaru 78

Tsohon Ministan Kasuwanci da Masana'antu, Jubril Martins-Kuye, ya mutu yana da shekaru 78


Tsohon karamin Ministan Kudi kuma Ministan Kasuwanci da Masana’antu, Sanata Jubril Martins-Kuye, ya mutu. Yana da shekaru 78. 


Marigayi Kuye ya mutu a gidansa da ke Victoria Garden City, Lagos a safiyar yau 17 ga watan Janairu. 


An haifeshi ne a watan Agusta 1942 a Ago Iwoye, mazabar Ijebu ta jihar Ogun yayi karatun kimiyyar zamantakewar al'umma a Jami'ar Ibadan (1965-1968) sannan kuma a fannin tattalin arziki a Harvard University Business, ya kammala a shekarar 1983. 


Ya sami cancantar zama Chartered Accountant. Ya kasance sanata a Jamhuriya ta Uku ta Najeriya. A 1999, an nada shi karamin Ministan Kudi a lokacin mulkin farko na Shugaba Olusegun Obasanjo, yana aiki har zuwa Yunin 2003. 


A watan Afrilun 2010, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi Ministan Kasuwanci da Masana'antu.


Majiya: Linda Inkejiblog


KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24

TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

0 Response to "Tsohon Ministan Kasuwanci da Masana'antu, Jubril Martins-Kuye, ya mutu yana da shekaru 78"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?