--
Tirkashi: Yadda Attajirin Duniya Aliko Dangote ya tafka asarar Naira Biliyan 350 a kwana 1

Tirkashi: Yadda Attajirin Duniya Aliko Dangote ya tafka asarar Naira Biliyan 350 a kwana 1


Aliko Dangote ya rasa kimanin Naira biliyan 350,100,000,000 a makon jiya Attajirin da ya mallaki $18.4bn a farkon mako, ya kare da $17.5bn a asusu 


Mai kudin ya sauko a jerin Attajiran Duniya daga na 106, ya koma na 114 Shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, Aliko Dangote, ya ga dukiyarsa ta yi kasa a ranar Juma’a, 8 ga watan Junairu, 2020. 


Jaridar Punch tace hakan na zuwa ne bayan kasa da kamfanin Dangote ya yi a kasuwar zuba hannun jarin Najeriya watau NSE. 


Bloomberg Billionaires Index wanda ta ke tattara alkaluman attajiran Duniya ta nuna Alhaji Aliko Dangote ya rasa Dala miliyan 900. Dangote wanda ya mallaki $18.4bn a ranar Alhamis, ya wayi gari ranar Juma’a da $17.5bn a asusunsa. 


Da wannan canji da aka samu, Dangote wanda shi ne attajiri na 106 a kaf Duniya kafin yanzu, ya koma na 114 a sabon jerin da aka fitar. Bayan ya samu karin Dala miliyan 600 a farkon kwanakin 2021, Aliko Dangote ya gamu da wannan babbar asarar cikin sa’o’i 24. 


Abin da hamshakin Attajirin Nahiyar Afrikan ya rasa a wannan takaitaccen lokaci a darajar kudin Najeriya, ya haura Naira biliyan 350. A tsakiyar Disamban 2020, dukiyar Dangote ta yi wani tashi daga Dala biliyan 15.5 zuwa dala 17.8, sama da Naira tiriliyan shida kenan. 


Har yanzu, Dangote ne kadai mutumin Najeriya da ya iya shiga jerin Attajirai 500 na farko da ake da su a Duniya, na farko a fadin Afrika. 


Legit

0 Response to "Tirkashi: Yadda Attajirin Duniya Aliko Dangote ya tafka asarar Naira Biliyan 350 a kwana 1 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?