--
Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji

Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji


Yan Boko Haram sun yi ikirarin kwace makaman jami'an tsaro - Daga cikin abubuwan da sukay ikirarin kwatowa akwai iga da harsasai Kungiyar masu tada kayar bayan Boko Haram a ranar Asabar ta saki sabon bidiyo dake nuna igwa, makamai da harsasan da mambobin kungiyar suka kwace a cikin dajin Sambisa, jihar Borno. 


Daya daga cikin yan ta'addan wanda yayi jawabi a bidiyo mai tsawon mintuna 4.15 yayi jawabi kan artabun da sukayi da Sojojin a dajin Sambisa ranar Juma'a, HumAngle ta ruwaito. Wata motar Igwa Vickers Mk.3 Eagle, harsasai igwa masu yawa da harsasan bindiga. 



Wannan na faruwa a lokacin da dakarun Sojin Najeriya suka kaddamar da atisayen Operation Tura Takai Bango inda suka farautar yan ta'addan ISWAO a dajin Alagarno- yankin Timbuktu. 


KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24

0 Response to "Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?