--
Na kashe shi ne don kare kaina - 'yar bautar kasa ta bayyana dalilin da ya sa ta kashe mutum har lahira a Akwa Ibom

Na kashe shi ne don kare kaina - 'yar bautar kasa ta bayyana dalilin da ya sa ta kashe mutum har lahira a Akwa Ibom


Princess Odume, ‘yar bautar kasan da aka kama bayan ta kashe wani mutum a Akwa Ibom a ranar Lahadi 10 ga Janairu ta bayyana dalilin da ya sa ta aikata hakan. 


Lokacin da ‘yan sanda suka yi mata tambayoyi bayan an kama ta, dm'yar bautar kasar da aka kama a lokacin da take kokarin tsallake wani shinge bayan ta kashe saurayin mai suna Japhet Akwaowo, an rawaito cewa ta aikata hakan ne don kare kanta. 


Kakakin 'yan sanda a jihar, Odiko Ogbeche-Macdon ya ce Odume ta yi ikirarin cewa Akwaowo ya yi mata barazanar kashe ta a kan ta ki amincewa da bukatar sa ta cire tufafinta don ya yi lalata da ita.


Macdon ya ce; "A zahiri ta kashe saurayin mai suna Akwaowo Japhet. Ta ce ta je sayan biredin wake, da akara, sai ta ga wani mutum da ke yi mata alama da ya zo gare shi. 


Ta ce ta je ta same shi, sun yi magana kuma ta tsinci kanta a cikin gidansa. "Ta ce ta jira shi a waje sai ya shiga ciki don kawo wuka. Ya ce zai soka mata wuka kuma ba wanda zai san abin da ya faru. Ta kuma ce Japhet ya nemi ta cire kayanta sai ta ki. Abin da ya faru a zahiri shi ne cewa ta fi karfinsa. "




0 Response to "Na kashe shi ne don kare kaina - 'yar bautar kasa ta bayyana dalilin da ya sa ta kashe mutum har lahira a Akwa Ibom"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?