ɓatan yara A Kano Mata sun yi zanga-zanga (Kalli Hoto)
Friday, 1 January 2021
Comment
Mata da dama a Jihar Kano sun fito sunyi zanga-zangar nuna damuwa kan yaransu da suka bata
Matan sun koka cewa yaransu kimanin 118 ne aka sace aka sayar a wasu sassan Najeriya tun shekarar 2016
Matan sun fito rike da takardu da kuma hotunan yaran sunyi tattaki zuwa hukumar karbar korafi da giajen watsa labarai
Matan da yaran su suka bata a Kano sunyi zanga zanga a Kano ranar Laraba akan abin da suka kira sakacin hukumomi wajen mayar da hankali don dawo musu da yaran su, Daily Trust ta ruwaito.
Matan rike takardu da banoni da kuma hotunan yaran da suka bata, sun kai ziyara hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa, ma'aikatar al'amuran mata da kuma gidajen jaridu don mika koken su.
Zainab Abdullahi Giginyu, ta ce, "mun gaji da wannan al'amarin. shekaru da dama muna korafi, amma gwamnati ta nuna halin ko in kula."
A cewar ta, daga 2016 zuwa yanzu, matar ta bayyana bacewar yara 118 kuma an yarda cewa sace su akayi aka siyar a wani bangaren kasar nan,
Ta ce mafi yawancin yaran sun fito ne daga unguwannin Hotoro, Kawo, Yankaba da Gama da ke jihar, ta na cewa "abun ya dame mu kwarai kuma muna son gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don ganin yaran mu sun dawo."
"Muna sane da kwamitin da gwamnatin ta kafa, amma bamu ji ko mun ga wani abu da suka dauka akan al'amarin ba", a cewar ta.
A jawaban da suka gabatar, kwamishinar mata ta jihar, Zaharau Mohammed da kuma shugaban hukumar karbar korafi, Barrister Muhuyi Rimin Gado,
sun tabbatar wa matan cewa gwamnatin jihar zata yi duk mai yiwuwa don ganin yaran su sun dawo cikin koshin lafiya
Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa lamarin batan yara ya dade yana addabar jihar, an taba kama wasu da ke da alaka da satar yaran kuma an gurfanar da su.
A watan Yunin shekarar da mu ke bankwana da ita, gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da kwamiti don su tattara bayani akan wasu yara da aka sata aka kuma siyar da su a jihar Amambra a 2019.
Source: Legit
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to " ɓatan yara A Kano Mata sun yi zanga-zanga (Kalli Hoto)"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?