Kayan Lefe: Matasa suna so ayi watsi da al’adar kai akwati, kayan gara da gyaran daki a Arewa
Lefe in itself should be cancelled, no point, most people don’t end up wearing half of it, marriage should be made easy as directed by Islam, kayan gida and gara should also be canceled. Young people should be allowed to start their life with the little they can. https://t.co/IwhaKZrI6q
— Safiyya Dattijo (@Safiyyah_Datti) January 3, 2021
“Haka zalika a soke kayan gida da gara. A bar sabon aure su fara rayuwarsu sannu a hankali.” Shi ma wani Bawan Allah mai suna Abdullahi UDK ya na da wannan ra’ayi, ya ce da sake. Ya ce lefe bai da wani amfani, kuma ba a bukatar shi.
a aure. “Manyan Arewa suna bukatar su zauna, su yi fatali da al’adar gayyatar mutane su zo kallon lefe. Bai jawo komai sai hassada da kuma kananan maganganu.”
Malam Abdullahi UDK ya kara da cewa ganin gidan amarya ya shiga ciki, a cewarsa babu alilin a rika shiga gida domin ganin irin kayan da aka jera a ciki.
Amma irinsu wata Ruqayyah Hayatey sun ce abin da ya kamata shi ne kwarya ta bi kwarya wajen aure, ta haka iyaye ba za su sha wahalar aurar da yara ba.
Wasu kuma sun kare yin lefe da ake yi, su ka ce idan ba don haka ba, akwai matan da ba za su rika sanya tufafin kirki bayan sun shiga gidan mazajensu ba. Kwanakin baya kun samu rahoto game da yadda kayan lefe ke hana aure a kasar Hausa.
Da yawa daga cikin su na kukan hada kayan lefe ke hana su yin aure a Arewacin Najeriya saboda tsabar kudi da a ke kashewa wajen hada kayan akwatin 'yan mata.
A wajen auren Hausa da Fulani, daya daga cikin batutuwan da suke tasowa wajen yin aure shine kayan lefe da namiji zai hadawa wadda ya ke neman auren na ta.
This is léfé 👇🏽 https://t.co/Mjx4bPiwsp
— The Prince (@AbdullahiUDK) January 4, 2021
Source: Legit
0 Response to "Kayan Lefe: Matasa suna so ayi watsi da al’adar kai akwati, kayan gara da gyaran daki a Arewa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?