
Kunsan Kasashen duniya 8 mafi karfin Soja a duniya a 2021 ? (Duba Jerinsu anan)
Kowace kasa na alfahari da adadin Sojojin da take shi da makamai - Yayinda wasu ke tunanin Amurka ta fi kowa karfi, kasar Sin ta zarce mata Wani jerin kasashe masu karfin Soja a duniya a 2021 da Global Firepower ta saki ya nuna cewa kasar Sin ne kan kan gaba wajen yawan jami'an sojoji, rahoton Statista ta bayyana.
Rahoton ya nuna cewa kasar sin na adadin Sojoji milyan 2.19 dake shirye da fuskantar yaki. Kasar da ta samu damar zuwa ta biyu itace Indiya mai adadin Sojoji milyan 1.45. Amurka ce ta zo na uku da Sojoji milyan 1.4, sannan sai kasar Koriya ta Arewa.
Ga jerin kasashe 8 mafi karfin Soja a duniya:
1. Sin: 2,185,000 2.
Indiya: 1,445,000 3.
Amurka: 1,400,000
4. Korea ta Arewa : 1,300,000
5. Rasha: 1,014,000
6. Pakistan: 654,000
7. Korea ta kudu: 600,000
8. Iran: 525,000
Jaridar Legit.ng ta lura cewa babu kasar Afrika ko daya cikin manyan kasashe 8 mafi karfin Soja. Amma a 2019, Sojojin Najeriya sun zo na hudu a jerin Soji mafi karfi a nahiyar Afrika.
A bisa rahoton da Global Firepower ya saki, Najeriya ta biyo bayan Misra, Aljeriya, da Afrika ta kudu. A duniya kuwa, Najeriya ta zo na 44 a shekarar 2019.
MAJIYA: LEGIT
KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI: https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:
FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24
TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
0 Response to "Kunsan Kasashen duniya 8 mafi karfin Soja a duniya a 2021 ? (Duba Jerinsu anan) "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?