--
Kotun Soji ta yankewa Sojan da ya kashe kwamandansa hukuncin kisa duba dalili

Kotun Soji ta yankewa Sojan da ya kashe kwamandansa hukuncin kisa duba dalili


Bayan watanni shida da aikata laifi, kotu ta yankewa soja hukuncin kisa  Kotun ta yankewa wasu sojin daban hukuncin dauri a gidan kaso kan wasu laifukan daban Kotun soji dake zamanta a Maidiguri, jihar Borno ta yankewa jami'in soja, Azunna Maduabuchi hukuncin kisa kan laifin kisan kwamandansa, Laftanal Babakaka Ngorji. Kotun ta yanke a kashe shi ta hanyar harbi, Channels Tv ta ruwaito. 


An gurfanar da Maduabuchi ne bayan da ya budewa Babakaka Ngorji wuta a watan Yulin 2020 a sansaninsu dake karamar hukumar Bama a jihar Borno don ya hanashi zuwa gida. Kotun dake Maimalari Cantonment, ta kamashi da laifin kisan kuma ta yanke masa hukuncin kisa. Sauran sojojin da aka kama da laifin kisa sun samu hukuncin dauri shekaru a gidan kaso. 


Wadanda aka yankewa hukumar sune Sajen Sani Ishaya, hukucin shekaru hudu; Bidemi Fabiyi, hukuncin shekaru biyu; sai kuma Private Musa Bala da Abdulrasheed Adamu, da aka yankewa hukuncin shekara daya. 


Wani Soja kuma mai suna Mohammed Kudu da aka tuhuma da laifin kashe wani yaro a wani bikin daurin aure ya samu daurin shekaru uku a gidan kaso. Hakazalika an ragewa Lance Kofura Aja Emmanuel matsayi kan laifin cin zarafi. Yanzu ya koma Private.



0 Response to "Kotun Soji ta yankewa Sojan da ya kashe kwamandansa hukuncin kisa duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?