--
Kotu ta yi fatali da hukuncin kisa da aka yanke wa wanda yayi sabo a kano duba lalinta anan

Kotu ta yi fatali da hukuncin kisa da aka yanke wa wanda yayi sabo a kano duba lalinta anan



Kotu ta soke hukuncin kisa da aka yanke wa Yahya Sharif Aminu, wani mawaki dan asalin jihar Kano da aka samu da laifin yin sabo.


A wani hukunci da babban alkalin jihar Nuraddeen Sagir ya gabatar a ranar Alhamis 21 ga watan Janairu, ya bayyana cewa shari’ar cike take da kura-kurai kasancewar ba a baiwa mai karar wakilcin sharia ba.


Sagir ya kuma ce hukuncin da kotun koli ta yanke ya sabawa sashi na 2-6-9 na dokar aikata laifuka.


Ya ba da umarnin cewa a sake yin shari’ar a waccan kotun sannan a bai wa mai shigar da kara adalci da kuma wakilcin lauya a karkashin wani alkalin. 


Ana tsare da Yahya sharif ne tun tsawon shekara guda sakamakon aikata sabo ta hanyar cin zarafin Manzan Allah {S.A.W} Dayayi acikin wata waqa dayayi kuma ya yadata a kafar sadarwa ta whatsapp:


KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24

0 Response to "Kotu ta yi fatali da hukuncin kisa da aka yanke wa wanda yayi sabo a kano duba lalinta anan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?