--
Ko kunsan dalilan dake sanya amarya kuka lokacin da za'a kaita gidan miji?

Ko kunsan dalilan dake sanya amarya kuka lokacin da za'a kaita gidan miji?


Dalilan dai kamar yadda galibin mutane ke fada suna da nasaba da kewar gida da 'yan matan ke tunanin yi da zarar sun bar iyayensu.


''Suna jin kunya da fargabar haduwa da wadanda ba iyayensu ba, da dangin da ba nasu ba, suna jin kunyar an hada su da wani namiji , kana suna ganin an raba su da iyayensu, da yan uwansu da kawayensu, zama dandali da suka saba, duk hakan na sa amare yin kuka,'' in ji Mai-Zabura.


Ya kara da cewa: ''A wasu lokuta ma nisa da gida ko garin da yarinya take shi yake kara sa amarya ta rika kuka, don za ta hadu da wata sabuwar rayuwa da ba ta saba da ita ba kuma a inda take fargabar za ta dade bata ga iyayenta da danginta ba.''


Hajiya Amina Saulawa da ke jihar Katsina ta shaida wa BBC cewa a baya yakan kasance a wasu lokutan ita yarinyar ba ta ma san wanda za a aura mata ba, don haka babu shakuwa a tare a tsakaninsu, shi ya sa yarinya kan rika kuka idan za a kai ta gidan miji.


"Amaren kan rika kuka ne saboda galibi wasu a lokacin ba su riga sun mallaki hankalinsu ba, saboda karancin shekaru, ba su fahimci mecec e rayuwar aure ba, sannan ga rabuwa da iyaye,'' in ji Amina.


Ita kuwa malama Rahinatu Abubakar cewa ta yi gaskiya zamanin da da na yanzu akwai bambanci sosai wajen al'adar kukan da amare ke yi lokacin da za a kai su gidan miji.


Rahinatu ta ce '' Dalilan da suka sa amarya ke kuka lokacin da za a kaita gidan miji sun hada da tsoron inda za a kai ta, don bata san me zata tarar ba, ga kuma alhinin rabuwa da iyaye''.


''Shekaruna 12 lokacin da aka yi min aure aka kai ni can garin Bidda jihar Niger, kuma bayan an kai ni na rika guduwa makabarta ina kwana, na ka tada kai da kabari in yi barci na,'' ta ce.


''Daga bisani da na ga alamu ana fako na sai na koma hawa kan bishiyar mangwaro ina kwana, don kawai ina gudun gidan miji,'' in ji ta.


Amma kuma ta ce yanzu lamarin ya sauya, sai dai kuma duk da haka akwai daidaikun wurare da har yanzu ake samun irin wannan al'ada ta kukan aure.


Wannan layi ne

Hakan na faruwa ne in ji ta saboda a yanzu ana barin yara mata su yi karatu mai zurfi wanda hakan yakan sa su kara mallakar hankalinsu kafin a yi musu aure.


Ta kuma kara da cewa ''Babban dalilin kukan shi ne saboda ka saba da gidanku, da mahaifanka, da 'yan uwanka, kuma ka san cewa idan ka tafi shikenan sai lokaci mai tsawo, kuma a wasu lokutan akan kai yarinya wani gari ne mai nisa.''


Ita ma a nata ra'ayin wata dattijuwa Hajiya Fatima Haruna cewa ta yi batun haka yake, yawanci kukan rabuwa da iyaye da dangi ne sassala, duk da cewa akwai sauran dalilai da kan sa kukan.


''Shekaruna 13 lokacin da aka yi mini aure, kuma iyayena ne suka zabar min suka ce sai Bafulatani dan uwana,'' in ji ta.


Ta kuma bayyana cewa a lokacin da aka kai ta gidan miji surukarta ce ta rika kula da ita, sai bayan wata daya sannan ta ga mijin da aka aura mata.

Sai dai kuma wasu dalilan da suka sa yanzu ba a cika samu irin wannan al'ada da kukan tafiya gidan miji ba shi ne saboda abubuwan sauye-sauye da zamani ya kawo wadanda suka hada da ci gaba a fannin sufuri, baya ga bunkasar hanyoyin sadarwa irin su wayar salula da kuma hanyoyi daban-daban da a ko ina kake a duniya kamar kana tare da mutum.


Malama Surayya Aminu wata matashiya ce da a shekarun baya aka yi mata aure, kuma ta shaida wa BBC cewa ita ba ta taba sanin ma akwai wata al'adar da ake kuka idan za a tafi gidan miji ba.


''Ni kam na sai bayan da na kusa kammala karatun jami'a aka yi min aure, na san babu dadi rabuwa da iyaye da 'yan uwa, amma kuma na san komai dadewa zan bar su, don haka mene ne abin kuka tun da auren soyayya muka yi?,'' in ji ta.


Ta kuma ce: ''Ai ko a ina ne tun da akwai kafofin sadarwa a koda yaushe ina iya magana da iyayena da 'yan uwana, ko da kuwa hira da bidiyo ne muna ganin juna kamar muna tare, don haka babu wata damuwa''.


Halima Sani kuwa ta cewa ta yi lokacin da aka yi mata aure na soyayya tana da shekara 21, amma duk da hakan sai da ta yi kukan rabuwa da iyayenta.


''Ina son mijin da aka aura min, auren soyayya ne, ina ta murna amma kuma ranar da za a kai ni gidansa sai da hankalina ya tashi, sai wani tunani ya zo min na ga cewa zan fara wata rayuwa da ban sani ba, kuma zan daina ganin iyayena, da 'yanuwana kamar yadda na saba,'' a cewarta.

MAJIYA: BBC HAUSA

READ MORE ARTICLES:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

DOWNLOAD OUR ANDROID APP: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

FOLLOW US ON:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24

TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

0 Response to "Ko kunsan dalilan dake sanya amarya kuka lokacin da za'a kaita gidan miji? "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?