--
Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Jihar Adamawa Duba dalilinsu

Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Jihar Adamawa Duba dalilinsu


A tsaunikan jihar Adamawa, wadanda suke kusa da kasar Kamaru, akwai kabilu daban-daban - Akwai wani yare mai suna 'Koma', wanda akalla mutane 62,000 ne suke jin yaren kuma suke yin sa da bin al'adunsa 


'Yan kabilar Koma suna tsananin riko da al'adu, sana'a da addininsu, don har yanzu wasunsu basu sanya sutturun zamani A tsaunikan jihar Adamawa, akwai wani yare mai suna Koma, wadanda suka ta'allake rayuwarsu akan al'adunsu. 


Suna da iyaka da Kamaru, kuma sun rabu kashi 3: Mazauna Saman Beya da Ndamti, Vomni da 'yan kwarin Verre. Kamar 'yan kabilar Efik dake kudu maso gabas a Najeriya, 'yan kabilar Koma sun rabu a siyasance; akwai kauyaku 21 na Koma a gefen Kamaru da tsaunin Atlantika, sai wasu kauyakunsu 17 dake gefen Najeriya. 


Akwai a kalla mutane 62,000 da suke jin yaren, kuma suke iya yin yaren, har da yan bangaren Nijar da Congo. Koma suna bin al'adunsu kwarai, har yanzu suna amfani da gishirin gargajiya (Mangul). Ba sa amfani da ashana, saidai su goga duwatsu har su yi wuta. 


Sannan ba sa amfani da mayukan girki idan ba na gargajiya ba, suna da kuma abinci irin nasu. Duk da dai wasu matasansu suna sanya kaya irin na zamani, amma har yanzu akwai wadanda suke amfani da ganye da fatocin dabbobi wurin rufe jikinsu. Matansu suna sanya kaya na fatar zaki da kuma ganyayyaki. 


Idan mace ta mutu, yaranta mata sune suke gadar dabbobin da take kiwo, gonarta, da ababen amfaninta na gida kamar sarkokinta, kayan kwalliyarta da sauransu. Sai dai suna daukar haihuwar tagwaye a matsayin masifa, idan ba kwannan ba, birne tagwaye suke yi da ransu. Mutanen Koma sun yi imani da Ubangijinsu wanda suke kira Zum ko Nu. 


Sannan suna kiran rana da wadannan sunayen. Idan mutum yana so Ubangiji ya amsa masa bukatarsa kamar ya bashi lafiya, arziki ko haihuwa yana aiwatar da wasu ayyuka. Suna kiran gidan Ubangijinsu da Ken, sannan akwai namiji mai kula da wurin wanda suke kira Kene-Mari , da mataimakinsa, Kpani. Sana'o'insu sun hada da noma, kiwo da farauta. Mata da maza suna sana'o'in kamar noma da kiwo, amma mata ba sa farauta. 



0 Response to "Kabilar da suke daukan haihuwar tagwaye a matsayin bala'i har yanzu a Jihar Adamawa Duba dalilinsu"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?