Harin 'yan bindiga akano 'yan sanda sun kama mutum 2biyu a jihar Kano
Rundudnar 'yan sandan jihar Kano sun yi nasar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da aikata fashi da makami Jami'an sun kwato wata mota a hannun 'yan fashin yayin wasu daga cikinsu suka gudu Rundunar 'yan sandan jihar sun bayyana cewa suna ci gaba da bincike don gurfanar da wadanda ake zargin,
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da kame wasu mutane biyu da ake zargi da fashi da makami. An kuma kwato wata mota da 'yan fashi da makamin suka kwace, yayin da suka kashe mai motar a jihar Kano, Daily Nigerian ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare, a kan titin gidan zoo, kusa da Shoprite lokacin da wadanda ake zargin ’yan fashi ne suka harbe direban motar mai suna Isa Hassan Abubakar da ke rukunin gidajen Rijiyar Zaki bayan sun fitar da shi da karfi.
Wani shaidar gani da ido ya ce maharan sun fara harbin iska don tsoratar da mutane kafin su sauka kan mutumin mai shekaru 50 a cikin farar motar Pontiac Vibe. “Lokacin da suka yi harbe-harben bindiga a sama, mutanen da ke kusa da kantin Shoprite da hasumiyar Al-Hamsad sun fara guduwa don tsriratar da ruwarsu.
"Yayin da rikici ya barke, sai na ga 'yan bindigar sun tunkari wannan mutumin a cikin motarsa, suka fitar da shi da karfi suka harbe shi a take ya fadi kasa maharan kuma suka shiga cikin motar," in ji ganau, wanda ya gwammace ba mai suna.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce 'yan sanda sun hanzarta kai dauki wurin bayan jin karar harbe-harben. Ya kara da cewa da isar su, sai suka fatattaki ‘yan bindigar, inda daga karshe suka yi watsi da motar suka gudu.
Mista Kiyawa ya kara da cewa 'yan sanda sun kuma garzaya da wanda aka harban zuwa asibiti inda ya mutu a yayin da ake yi masa magani. Ya ce an kama biyu daga cikin wadanda ake zargin 'yan fashin ne yayin da ake ci gaba da bincike.
LEGIT
0 Response to "Harin 'yan bindiga akano 'yan sanda sun kama mutum 2biyu a jihar Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?