Kowane lokaci daga yanzu Gwamnatin tarayya na iya dakatar da rijistar lambar shaidar dan kasa da ke gudana afadin kasar
Gwamnatin tarayya na iya dakatar da rijistar lambar shaidar dan kasa da ke gudana.
Dokta Olorunnimbe Mamora, karamin ministan lafiya ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.Ya ce wannan shawarar ta biyo ne sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar Covid-19 a kasar.
Ya zuwa jiya, Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta tabbatar da adadin masu kamuwa da cutar mutane 100,087. kuma akalla 1358 aka ruwaito sun mutu tun lokacin da Coronavirus ta afkawa Najeriya a watan Fabrairu, 2020. Hakanan, kimanin mutane 80,030 aka ba su magani kuma aka sallame su.
A ranar Lahadi 10, 2021, NCDC ta tabbatar da sabbin kamuwa da cutar 1,544 na Coronavirus (COVID-19) a kasar.
Wannan duk da haka kira ne na farkawa ga duk dan Nijeriya cewa Covid-19 gaske ce. saboda haka aka samar da wata hanya don dakile yaduwar cutar, Mamora yayin da yake gabatar da fira a shirin Sunrise Daily na Channels Television a yau, ya ce zai zama hikima idan aka dakatar da rajistar NIN da ake gudanarwa a fadin kasar baki daya.
Kalamansa: “Ban ji daɗin kallon hoton ba inda mutane suka taru da yawa;
Amma kuma ina sane da cewa ma'aikatar da ta dace wacce ita ce sadarwa da tattalin arzikin dijital tana kallon wannan.
“Abin da na fahimta shi ne cewa za a iya dakatar da dukkan ayyukan ta yadda za a sake tsara yadda lamarin zai kasance game da yadda za a gudanar da taron saboda ba a taba tunanin zai zama haka ba.
“Muna da aiki a matsayinmu na gwamnati mu tabbatar da cewa mutane sun kare; muna kuma da aikin tabbatar da cewa mutane sun yi aiki da iyakar abin da zai amfani al'umma gaba daya. "
0 Response to "Kowane lokaci daga yanzu Gwamnatin tarayya na iya dakatar da rijistar lambar shaidar dan kasa da ke gudana afadin kasar"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?