Dubunsa ta cika: Yayi Shekaru 5 yana sayarwa da mutane mushen kaji a Maiduguri, {Kalli Hotunansa
Ya bayyana cewa ya shiga yin haka ne tun lokacin da mahaifinsa ya rasu Wani mutum mai suna, Hassan Ebere, ya bayyana yadda ya sayar da mushen kaji sama da 6,000 ga al'ummar Maiduguri tsawon shekaru biyar yanzu domin neman kudin ciyar da kansa.
Ebere ya bayyana hakan ne yayin magana da kamfanin dillancin labarai (NAN), bayan jami'an NSCDC suka damkeshi ranar Laraba a jihar Borno. "Na kan je rafin Ngadabul, bayan gidan talabijin BRTV, inda nike daukan mushen kajin da gidajen gona suka jefar, " ya bayyana. "Kowani mako, na kan dauki guda goma ko fiye da haka, sannan in gyara kuma in sayarwa mutane."
KU KARKUKARANTA: Gaskiya na gaji da boyewa, miji nike bukata - Kyakkyawar budurwa ta koka
"Kasuwannin da nake sayarwa sune kasuwar Kifin Baga, kasuwar Monday Market, shagunan masu Suya, da gidajen abinci, a cikin gari." "N700 zuwa N800 nike sayarwa. Amma idan suka kai yan kwanaki (ban sayar ba), na kan kai gidajen giya a bayan Ngomari in sayar da su N250," ya kara. Ebere ya ce shaidan ne ya tura shi aikata wannan abu kuma yana rokon a yafe masa.
Shugaban hukumar NSCDC na jihar Borno, Abdullahi Ibrahim, ya ce an damke mutumin ne yayinda yake gyaran kajin a bayan gidan talabijin da rediyo na BRTV ranar 2 ga Junairu, 2021
Kalli Hotunan:
0 Response to "Dubunsa ta cika: Yayi Shekaru 5 yana sayarwa da mutane mushen kaji a Maiduguri, {Kalli Hotunansa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?