--
Daga Qarshe Kotu ta bawa gidan yarin Kaduna umarnin gaggauta sakin matar Sheikh Zazaky

Daga Qarshe Kotu ta bawa gidan yarin Kaduna umarnin gaggauta sakin matar Sheikh Zazaky




Babbar kotun Kaduna ta umarci mahukuntan gidan yarin Kaduna su saki Zeenat, matar Sheikh El-Zakzaky domin a duba lafiyarta 


A makon jiya ne Mohammed, dan Sheikh Zakzaky, ya sanar da cewa mahaifiyarsa, Zeenat, ta kamu da cutar korona amma an hana fita da ita zuwa cibiyar killacewa 


Lauyan Sheikh El-Zakzaky, Femi Falana, ya gabatar da sakamakon gwaji da takardun asibiti da suka nuna Zeenat na bukatar kulawa saboda yanayin lafiyarta Wata babbar kotu da ke Kaduna ta umarci hukumar gidan yarin Jihar ta gaggauta sakin Zeenat, matar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban darikar 'yan uwa Musulmai na Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da ''Shi'a''. 


Kotun ta bayar da umarnin ne domin a mayar da Zeenat zuwa cibiyar killace masu cutar korona bayan tabbatar da cewa ta kamu da kwayar cutar. 


A hukuncin da ta yanke ranar Litinin, kotun ta bayar da umarnin a gaggauta mayar da Zeenat zuwa cibiyar killacewa mallakar gwamnati domin ta fara karbar maganin cutar korona.


A makon jiya ne dan Sheikh Zakzaky, Mohammed, ya sanar da cewa mahaifiyarsa, Zeenat, ta kamu da kwayar cutar korona a gidan yarin Kaduna amma mahukuntan gidan sun ki sakinta domin a duba lafiyarta. 


Tun shekarar 2015 gwamnati ta tsare El-Zakzaky tare da matarsa biyo bayan wata arangama a tsakanin magoya bayan IMN da dakarun rundunar soji a garin Zaria, Jihar Kaduna. Femi Falana, lauyan El-Zakzaky, ya gabatar da takaradun sakamakon gwajin Zeenat da sauran takardun asibiti da suka tabbatar da cewa tana bukatar kulawa ta musamman saboda yanayin lafiyarta. 


Babban lauyan, mai lambar 'SAN', ya roki kotun ta yi la'akari da shaidun da ya gabatar wajen bayar da umarnin sakin Zeenat domin ta samu kulawa a cibiyar killacewa kamar yadda hukumar NCDC mai yaki da cututtuka ta tsara tun bayan barkewar annobar korona. 

MAJIYA: LEGIT.NG

KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24

0 Response to "Daga Qarshe Kotu ta bawa gidan yarin Kaduna umarnin gaggauta sakin matar Sheikh Zazaky "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?