--
Cizon da Mage tayi matane yayi sanadiyyar mutuwarta - Inji Uwar Dakin Yarinya 'yar shekaru 16 data mutu a kano

Cizon da Mage tayi matane yayi sanadiyyar mutuwarta - Inji Uwar Dakin Yarinya 'yar shekaru 16 data mutu a kano


An cigaba da saka da warwara a jihar Kano bayan mutuwar wata 'yar aiki mai shekaru 16 bisa dalilin mutuwarta 


Duk da dai wata wacce suke aiki tare ta sanar da yadda wacce suke yi wa aiki tayi mata duka har ta kai ga ta kasa tashi ta mutu 


Duk da dai wasu sun ce cizon mage ne yayi sanadiyyar mutuwar yarinyar, don wacce take yi wa aiki ta ce daga baya ta san ta mutu An cigaba saka da warwara bayan mutuwar wata mai aiki 'yar shekara 16 a Kano, inda mutane da dama suka yi ta bayar da bayanai akan mutuwar ta. 


Wacce suke aiki tare ta sanar da Daily Trust cewa wacce suke yi wa aiki ce tayi ta dukanta har sai da ta mutu. 


'Yan sanda kuma sun sanar da yadda suka samu labarin cewa cizon mage ne yayi sanadiyyar mutuwarta, kamar yadda matar da ake zargi ta sanar. 


Al'amarin ya faru ne a Sharada Salanta wuraren tsakiyar Kano a ranar bayan matar ta koma gida ta ga yarinyar, Khadija Rabi'u, bata yi ayyukanta ba. 


An rufe gidan da lamarin ya faru a ranar Alhamis. Yanzu haka matar da ake zargin ta daki Khadija har ta yayi sanadiyyar mutuwarta ta barbada mata yaji a al'aurarta tana hannun 'yan sanda. 


Wata ganau, Rafi'a Muhammad, wacce itama 'yar aikin matar ce ta sanar da Daily Trust cewa matar ta bukaci ta taya ta dukan marigayiya Khadija. Rafi'a tace sun koma gidan tare da Khadija inda wacce suke yi wa aiki ta tambayeta dalilin da ya sanya bata yi ayyukanta ba, inda tace bata da lafiya.



Take anan ta fara ta dukanta har ta gayyatar ta don ta taya ta. Ta fara taya ta dukan bayan matar ta gama zaginta, sai ta lura numfashinta ya fara daukewa. 


Matar ta cigaba da dukanta har da sanya mata wani karfe a al'aurarta, daga nan ta bada mata yaji a al'aurar. Bayan ganin numfashinta ya dauke ne ta kai ta asibiti su kuma suka ki amsarta sai ta kawo dan sanda. 


Malama Ummalkhairi Shehu da tayi wa gawar Khadija wanka ta bayyana yadda duk jikinta yayi kaca-kaca da ciwuka. Amma kakakin 'yan sanda, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce ana zargin cizon magen da yayi sanadiyyar mutuwarta 


READ MORE ARTICLES:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

DOWNLOAD OUR ANDROID APP: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

FOLLOW US ON:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24

TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

0 Response to "Cizon da Mage tayi matane yayi sanadiyyar mutuwarta - Inji Uwar Dakin Yarinya 'yar shekaru 16 data mutu a kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?