
'Bullar wani faifan bidiyo da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
Bidiyon wasu yan Najeriya ya shahara a shafin soshiyal midiya inda aka gano su suna watsa bandir din kudi a kogi
Mazajen sun wanke fuskokinsu a cikin ruwan kazantan wanda masu amfani da shafin sadarwar ke ganin asiri suke yi da nufin habbaka arzikinsu
Daya daga cikin wadanda suka yi martani kan bidiyon ya ce a koda yaushe iblis kan wahalar da wanda ya mallakawa dukiya Wani bidiyo ya shahara a shafin soshiyal midiya na wasu da ake zaton yan damfara ne suna watsa bandir din kudi a kogi.
Yan Najeriya a shafin soshiyal midiya na ganin cewa abunda suka aikata asiri ne da nufin bunkasa arzikinsu. A bidiyon, an gano mazan su hudu suna
Yan Najeriya sun je shashin sharhi na bidiyon wanda @lindaikejiblogofficial ta wallafa a Instagram.
@officialbecks ta ce: “Suna biyan shaidan bashin abunda yake nashi.” @iamvictoria_richard ta ce: “Idan arzikinka ba na Allah bane, shaidan zai ta wahalar da kai a koda yaushe.”
@angelsvirginhair_ ta rubuta: “Ta Yaya hakan ya zama asiri?? Allah ya kyauta. Kamar yadda kuka yarda da Annabi Isah sannan kuke zuwa coci da sadaka, sauran ma suna da nasu al’adan da suke ba abun bautar su. Wannan ba tsafi bane.”
Majiya: Legit
KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:
FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24
TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice
0 Response to "'Bullar wani faifan bidiyo da ke nuna wasu yan damfara suna watsa bandir din kudi a kogi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?