--
Kalli Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' wanda ya janyo cece-kuce

Kalli Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' wanda ya janyo cece-kuce




Bidiyon mai martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ya janyo cece kuce a dandalin sada zumunta 


An hoton bidiyon da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna shi tare da matan zumunta suna wakokin addini 


Mutane da dama sunyi ta bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon inda wasu suka yabe shi wasu kuma akasin haka Wani hoton bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya janyo hankulan 'yan Najeriya musamman masu amfani da Twitter. 


A cikin bidiyon, An gano Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleiman Adamu, yana rere wakokin yabo na addinin kirista tare da 'matan zumunta' a yayin da suka kai masa ziyara fadarsa 


Kungiyar fitaciyyar kungiya ce ta masu waka a Kiristocin arewacin Najeriya da aka san su da iya rere wakokin addinin kirista masu ratsa zuciya. Isa Gusau, babban sakataren watsa labarai na gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum, ne ya wallafa bidiyon kuma a halin yanzu fiye da mutane 1000 sun latsa alamar so kan bidiyon. 


Ba a san tabbacin ranar da aka nadi bidiyon ba amma a garin Gusau aka dauka kamar yadda fitaccen manhajar sadarwa ta WhatsApp ta nuna. 


 

Dakta Adamu shine sarki na 11 a masarautar Bauchi kuma sarki mai ci a yanzu. Ya yi karatun digirin farko a Fasahar Gini daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. 


Wasu da dama sun yaba wa abinda sarkin ya yi inda suka ce hakan na iya hada kan al'ummar jihar da kasa baki daya. 

 

Source: Legit

Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kalli Bidiyon Sarkin Bauchi yana waƙar kiristoci tare da 'matan zumunta' wanda ya janyo cece-kuce"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?