Babbar magana: Wani dan kasuwa ya maka surukinsa a kotu a kan N69,000
Wani dan kasuwa ya kai karar surukinsa kotu da zargin kin biyansa hakkinsa N69,000 Dan kasuwan ya bayyana cewa surukin nasa yazo har shago ya karbi kaya wa matarsa
Bayan sauraran kara, alkali ya bukaci mai gabatar da kara ya kawo shaidunsa gaban kotu Wani dan kasuwa, Abdulkadir Oyeleke, a jiya, ya maka surukinsa, Malam Sani, a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Magajin Gari, Jihar Kaduna, yana neman a karbo masa N69,000, Vanguard News ta ruwaito.
Oyeleke ya fadawa kotun cewa a watan Janairun shekarar 2020, matar Sani, wacce kanwarsa ce, ta ziyarce shi a shagonsa sai ta ga wasu dinkakkun kaya masu kyau kuma ta gaya masa cewa mijinta yana sha'awarsu. Oyeleke ya ce:
“Lokacin da Sani ya zo, ya zabi saiti hudu kan N10,000 kowanne. Ya zabi wasu guda biyu, wanda kudin su yakai N4,000 kowannensu sannan ya sayi turaren hammata dayOyeleke
“Yanzu wata uku kenan. Bai biya ni bashin da nake binsa ba. Ya kuma roke ni in ba shi rancen N20,000 kuma na bashi. “Sani ya daina daukar wayata ko amsa sakonni.
Ina rokon kotu da ta umarci Sani da ya biya ni kudina.” Wanda ake kara, Sani, mai buga takardu wanda ke zaune a cikin garin Kaduna, ya musanta zuwa shagon Oyeleke.
Sani ya ce "Matata ta kawo kayan sannan ta tilasta ni na sayi kayan dan uwanta." Sani ya kuma musanta karbar N20,000 na Oyeleke.
Bayan sauraron bangarorin biyu, alkalin kotun, Murtala Nasir, ya umarci mai shigar da karar da ya gabatar da shaidu don bayar da shaidar cewa wanda ake tuhumar ya yi alkawarin ba shi wani kudi na tufafi. Nasir ya dage sauraron karar har sai 28 ga watan Janairu don ci gaba.
MAJIYA LEGIT
KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:
FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24
0 Response to "Babbar magana: Wani dan kasuwa ya maka surukinsa a kotu a kan N69,000 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?