
Ba zamu kulle makarantun jihar Kano ba, gwamna Ganduje
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce ba zai kyautatu a rufe makarantu domin hana yaduwar cutar Korona ba a jiharsa. A cewar jawabin da sakataren yada labaran Ganduje, Abba Anwar, ya saki, ya ce gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a wata ganawa da kungiyar malaman Najeriya (NUT).
Ganduje ya ce rufe makarantu zai janyo koma baya a harkar ilimi saboda hakan ba zai hana yara kamuwa da cutar Koronan ba. "Akwai bukatar yaki da annobar, amma mutane su fahimci illar wasu abubuwan da sukeyi," yace.
"Matsalan ba rufe makarantu bane. Idan ka rufe makarantu, wani hadarin ne, saboda idan kuka kulle makarantu da niyyar hana dalibai kamuwa da COVID-19, wannan cutar na iya kamasu a gidajensu." "Rufe makarantu zai zama koma baya ga daliban da kuma harkar ilimi.
Shi yasa muka ki umurtan malamai su zauna a gida, sabanin ma'aikatan gwamnati da muka umurta suyi zamansu a gida." A cewar NAN, gwamnan ya ce jihar za ta samar da wasu hanyoyi na daban domin dakile yaduwar cutar.
KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:
FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24
0 Response to "Ba zamu kulle makarantun jihar Kano ba, gwamna Ganduje"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?