--
Ankulle cibiyar lafiya gabadayanta a legas duba dalili

Ankulle cibiyar lafiya gabadayanta a legas duba dalili


An rufe cibiyar kiwon lafiya a matakin farko ta Meiran da ke yankin karamar hukumar Agbado / Oke-Odo a jihar Legas bayan da wasu ma’aikatan kiwon lafiya suka kamu da kwayar cutar Corona.


An bayyana hakan ne a wata sanarwa da Mosunmola Olabige, babban sakataren yada labarai na David Famuyiwa, shugaban Agbado / Oke-Odo ya saki a ranar Lahadi, 10 ga Janairu.


Duba Bayani A ƙasa;


“A cikin hanzarin Akai dauki don dakile yaduwar kwayar cutar Corona a cikin al’umomin, Shugaban Agbado / Oke-Odo LCDA ya ba da umarnin rufe cibiyar lafiya ta matakin farko ta Meiran.


Wannan ya zama dole ne yayin da wasu daga cikin ma'aikatan cibiyar kiwon lafiya suka kamu da mummunar cutar korona.


Shugaban ya kuma bayar da umarnin a fara gano abokan aikinsu gami da marasa lafiyar da suka ziyarci wurin a kwanakin da suka gabata.


Ya kuma yiwa membobin al'umma nasiha game da kula da lafiyarsu da rayukansu ta hanyar guje wa tarurrukan zamantakewar da ke jawo manyan tarurruka, da kuma bin ka'idojin da aka shimfida kan amfani da abin rufe fuska, wanke hannu a kai a kai domin kaucewa kamuwa da cutar,


DAGA: Bz News24/7

0 Response to "Ankulle cibiyar lafiya gabadayanta a legas duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?