An kama wasu mutane uku da ake zargi 'yan damfara ne ta intanet tare da wasu 14 a Legas (Kalli hotuna)
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an kame wadanda ake zargin ne a ranar Talata, 26 ga watan Janairu, da Laraba 27, 2021 a wurare daban-daban biyo bayan jerin bayanan sirri da ke bayani kan zargin da ake musu na zamba ta intanet da sauran laifuka masu nasaba da hakan a Najeriya da kasashen waje.
"Wadanda ake zargi da zama a Dubai wadanda aka kama a Victory Nest Estate, Jakande, Lekki, Lagos a yau 27 ga Janairun 2021. su ne; Joshua, Adeyemo Olatunde, Solomon Emelike, Lawrence Nw, odu da Philip Olamilekan. "
“Sauran wadanda ake zargi wadanda aka cafke a 41c, Muritala Eletu Osapa London, Lekki yankin Legas a ranar Talata, 26 ga Janairu, 2021 sun hada da Ogbenusi Ibrahim, Kelechi Collins Ndubuka, Sadiq Adewale, John Okafor Eze, Adewale Lateef, Hassan Mohammed, Tunde Lawal da Hussaini Adebayo. "
A cewar EFCC, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zaran an kammala bincike.
MAJIYA LINDA INKEJI BLOG
KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:
https://www.bzglobalservice.com.ng/
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI:
https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7
KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:
FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24
0 Response to "An kama wasu mutane uku da ake zargi 'yan damfara ne ta intanet tare da wasu 14 a Legas (Kalli hotuna)"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?