--
An kama wasu mata biyu da laifin zubawa 'yar aikinsu mai shekaru 10 ruwan zafi a jihar Anambra

An kama wasu mata biyu da laifin zubawa 'yar aikinsu mai shekaru 10 ruwan zafi a jihar Anambra


Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Anambara ta cafke wasu mata biyu, Nneka Ayaene, mai Shekaru 34, da Chinenye Okoh, mai Shekaru 22, A garin Ndiowu a karamar hukumar Orumba ta Arewa da ke jihar ta Anambra bisa laifin kona wata yarinya ‘ yar shekara 10, Chidinma Nworie. 


Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Moammed Haruna ya fitar ta ce an kama wadanda ake zargin ne a ranar 5 ga watan Janairu daga ofishin ‘yan sanda na Oko da aka kama bayan wani korafi da mazauna yankin suka gabatar na cewa wadanda ake zargin sun ci zarafin 'yar Aikin gidansu ta hanyar watsa mata Ruwan zafi.



wanda yayi sanadiyyar raunata ta a duk ilahirin jikinta. Haruna ya ce wadanda ake zargin sun far wa karamar yarinyar ne saboda ta kasa jira ta dawo da kwanon ruwan da ta kawo wa wadanda ake zargin.


Kakakin yan sandan ya ce an garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Mafi kyau na Oko domin kula da lafiyar ta inda yanzu haka take karbar magani.


Ya ce an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotun majistare dake  Nanka kuma an daga karar zuwa ranar 2 ga Fabrairu. Haruna ya ce an tsare wadanda ake zargin a Cibiyar Gyara da ke Onitsha.



0 Response to "An kama wasu mata biyu da laifin zubawa 'yar aikinsu mai shekaru 10 ruwan zafi a jihar Anambra "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?