--
Abin nema yasamu Gwamnatin tarayya ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin katin shaidar 'dan kasa

Abin nema yasamu Gwamnatin tarayya ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin katin shaidar 'dan kasa


Ma'aikatar sadarwa ta bai wa kamfanonin sadarwa lasisin yiwa 'yan Najeriya rajistan NIN Ma'aikatar an bayyana ta duba ne da korafin ma'aiktan NIMC na yawan cincirindo da suke fuskanta a ofisoshinsu Sai dai har yanzu ma'aikatar ba ta kara wa'adin da a ka bayar na rufe rajistan ba 


An bai wa kamfanonin sadarwa lasisin yin rajistar mutanen da ba su da Lambobin Shaidar zama dan Kasa don rage dumbin jama’a a ofisoshin Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa, in ji NIMC. 


Darakta-Janar na NIMC, Aliyu Aziz, ya ce wasu sauran kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati su ma hukumar ta ba su lasisi don samar da NINs domin magance cincirindon jama’a a ofisoshin hukumar. 


Wannan ya zo ne yayin da ma’aikatan hukumar suka fada a ranar Talata cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami, ya kafa kwamiti don magance bukatun ma’aikatan NIMC. 


Da yake amsa tambayoyi game da matakan da NIMC ta dauka dangane da korafin da ‘yan kasa da kuma cincirindon jama’a a ofisoshin hukumar, Aziz ya ce an bai wa kamfanonin sadarwa na wayar salula ikon bayar da lambobin na ainihi. 


"Mun ba da lasisi ga kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati da suka hada da telcos (kamfanonin sadarwa) don samar da wasu cibiyoyi," kamar yadda ya bayyana a cikin sakon WhatsApp ga wakilin PRNigeria. 


MAJIYA LEGIT


KUKARANTA SABBIN LABARAI ANAN:

https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR HANNU KYAUTA A WAYOYINKU DOMIN SAMUN SABIN LABARAI: 

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

KUBIYOMU A SHAFUKAN SADARWA:

FACEBOOK: https://web.facebook.com/bzlabari24


0 Response to "Abin nema yasamu Gwamnatin tarayya ta bai wa MTN, Airtel, da sauran wasu kungiyoyi lasisin yin katin shaidar 'dan kasa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?