Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo
Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya caccaki Jam'iyyar APC a kan zarginsa da zama jagoran ta'addanci a arewa maso yamma - A cewar gwamnan, wannan kame-kame ne kawai, maimakon a yaba masa sai kuma zargi ya shigo, hakan ba adalci bane
Ya ce ba a ga kokarinsa da dagewarsa ba na fiye da sa'o'i 100, inda ya tsaya tsayin-daka wurin ceto daliban GSSS Kankara Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.
Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma. Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.
Kamar yadda yace, abin ban mamaki shine yadda babu kunya ba tsaron Allah, za a zarge shi da bata lokacinsa da kokarinsa har na tsawon sa'o'i 100, wurin tabbatar da an sako yaran. Ya ce:
"Wannan al'amarin yayi shige da na wata takarda da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya taba saki kwanakin baya, lokacin da gwamna Matawalle ya dage wurin ceto yara 26 na karamar hukumar Faskari, na nan jihar Katsina."
"Gwamna Matawalle ya dage wurin ganin ya kawo karshen ta'addanci a jiharsa. Kuma shugaba Buhari kullum cikin yaba masa yake yi. Yanzu haka jihar Zamfara tafi wasu makwabtanta zaman lafiya. Kuma ya yi alkawarin dagewa wurin ganin karshen ta'addanci a jiharsa.
"Gwamnan ya bukaci duk masu ruwa da tsaki, da su hada kai, kuma su yi kokarin kawo mafita a kan harkar tsaron da take addabar arewa."
Source: Legit
0 Response to "Zargin daukan nauyin 'yan bindiga: Matawalle ya yi wa APC wankin babban bargo "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?