Zanga-zanga ya barke a Fatakwal bayan dan sanda ya bindige direban Keke-Napep kan N100 (Kalli Bidiyo)
Rikici ya barke a unguwar Rokpoku na birnin Fatakwal sakamakon bindige direban a-daidaita-sahu (Keke Napep). Wannan abu da ya faru misalin karfe 7 na safiya Alhamis, a hanyar tashar jirgin sama ya haddasa rikici a yankin. Wasu fusatattun matasa da abokan direban sun toshe hanyar suna zanga-zanga. Wani mai idon shaida ya ce dan sandan ya kashe direban ne saboda ya ki bashi na goron N100 da ya bukata.
The Cable ta ce kakakin hukumar yan sandan jihar, Nnamdi Omooni, ya tabbatar da hakan nda yace an damke jami'in da yayi kisan. "Ina sane da abinda ya faru a Rukpokwu. Daya daga cikin jami'anmu ya kashe wani matukin keke da safen nan. An kwace makamin dan sandan kuma an tsareshi yanzu," yace. "Mun tura mazajenmu wajen domin kwantar da kuran da kuma hana barkewar rikici."
"Muna kira ga mutane sun kwantar da hankulansu, su bari mu hukuntashi." "Kisan dans anda ko kona ofishin yan sanda ba zai dawo da wanda aka kashe ba; inamma hakan munanan abu zai yi." Wannan na zuwa watanni biyu bayan zanga-zangar EndSARS ta barke a Najeriya.
Police kill a tricycle (Keke) driver over #100 in
— Gossip_reel (@gossip_reel) December 10, 2020
Rukpokwu#EndPoliceBrutality#EndSARS #LekkiMassacre CNN and BBC
Bridget Bema #EndSarsNow Kiki NASS President #NationalAssembly #EndPoliceBrutalityinNigeraNOW pic.twitter.com/yflmPbrFdQ
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Zanga-zanga ya barke a Fatakwal bayan dan sanda ya bindige direban Keke-Napep kan N100 (Kalli Bidiyo)"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?