
Zaben kananan hukumomi a Kano: Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu, ra'ayi ya banbanta
Jam'iyyar PDP mai hamayyya ta rabu gida biyu a jihar Kano a yayin da zaben kananan hukumomi ke karatowa - Hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC) ta tsayar da ranar 16 ga watan Janairu a matsayin ranar zaben kananan hukumomi
A ranar Talata ne tsagin Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP ya sanar da cewa ba za su shiga a fafata da su a zaben ba Mambobin jam'iyyar PDP ma su biyayya ga Ambasada Aminu a Kano sun nesanta kansu daga sanarwar janyewa daga shiga zaben kananan hukumomi da za'a yi a jihar a cikin watan Janairu na shekarar 2021.
A ranar Talata ne shugaban riko na PDP a Kano, Dakta Danladi Abdulhameed, ya sanar da cewa jam'iyyar ba za ta shiga zaben kananan hukumomin da za'a yi ranar 16 ga watan Janairu ba saboda rashin yarda da hukumar zabe ta jihar Kano.
Sai dai, dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Dala a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Mustapha Mai Royal, ya sanar da Daily Trust, yayin hirarsu ta waya, cewa Dakta Abdulhameed kakakin darikar Kwankwasiyya ne ba na PDP ba.
"Kakakin tafiyar Kwankwasiyya ne ba na jam'iyyar PDP ba. Ambasada Aminu Bashir Wali ne jagoran jam'iyyar PDP a Kano," a cewar Mai Royal yayin da ya ke magana a kan sanarwar janyewa daga shiga zaben.
"Jam'iyyar PDP ba kungiyar Kwankwasiyya ba ce, a saboda haka a shirye mu ke mu shiga zaben da za'a yi ranar 16 ga watan Janairu. Ina magana ne da yawun Aminu Wali. Mun yi magana da shi bayan fitar waccan sanarwa kuma ya umarci mu sanar da mambobinmu su shiga zaben," a cewarsa.
A cewar Mai Royal, tsagin Aminu Wali na jam'iyyar PDP na da 'yan takara a dukkan kananan hukumomin Kano 44 kuma za su mika takardunsu na takara ga hukumar zabe ta jihar Kano (KANSIEC).
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Zaben kananan hukumomi a Kano: Jam'iyyar PDP ta dare gida biyu, ra'ayi ya banbanta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?