Zabarmari: An sake gano sabbin gawarwaki 35 har sun fara kumbura
Tuesday, 1 December 2020
Comment

An sake gano wasu sabbin gawarwaki 35 a yankin Zabarmari, jihar Borno, a cigaba da neman gawar manoman da aka kashe - A ranar Asabar ne mugayen 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram suka shiga gonakin kauyen Zabarmari tare da tafka muguwar barna
Ba tare da girmama rai ko rayuwar dan adam ba, mayakan Boko Haram sun daure manoman, sun yankasu, sannan sun kone gonakinsu Tawagar hadin gwuiwa ta sojoji da fararen hula (CJTF) sun sake gano karin akalla gawarwaki 35 da suka fara kumbura a yankin Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno.
Sabbin gawarwakin 35, wadanda aka gano ranar Litinin, daban su ke da 43 da aka yi jana'izarsu, hakan ya sauya alkaluman mutanen da aka tabbatar an kashe zuwa mutum 78.
Jaridar HumAngle ta rawaito cewa tawagar da ta gano gawarwakin ta binnesu nan take saboda ba za'a iya motsa su daga wuraren da suka fara rubewa ba.
A ranar Lahadi ne gwamnan jihar Borno, Babagana Umar Zulum, ya jagoranci jana'izar gawarwaki 43 na manoman da aka fara samun rahoton cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun yi wa yankan rago.
A ranar Asabar ne rahotanni suka bayyana cewa ƴan Boko Haram sun shiga ƙauyen Zabarmari, sun bi manoma har gonakinsu tare da hallakasu ta hanyar yi musu yankan rago.
Zabarmari kauye ne mai nisan kilomita 20 kacal daga hedikwatar rundunar atisayen Lafiya Dole wacce ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Majalisar dinkin duniya (UN) ta rawaito cewa a kalla mutane 110 aka kashe, lamarin da ke nuni da cewa an samu karuwar adadin mutanen daga 43 da aka rahotanni suka fara sanarwa.
Ana zargin cewa bayan kisan manoman, mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da mata ma su yawa. "Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a kan fararen hula maza da mata yayin da suke girbe amfanin da suka shuka a gonakinsu," a cewar Edward Kallon, shugaban ayyukan UN na ceto a Najeriya.
."Wannan shine hari mafi girma da mayakan Boko Haram suka kaddamar a kan fararen hula a cikin shekarar nan. Ina kiran a tabbatar da cewa wadannan miyagu sun shiga hannu domin su fuskanci hukunci," kamar yadda Kallon ya bayyana a cikin jawabin da ya fitar ranar Lahadi.
SOURCE: LEGIT
Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐
1GB @N350
2GB @N700
3GB @N1,050
4GB @N1,400
5GB @N1,750
Validity For 30Days
Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Zabarmari: An sake gano sabbin gawarwaki 35 har sun fara kumbura"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?