--
'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure

'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure

Matar aure ta koka da yadda 'yar uwarta ta yi wuff da mijinta daga zuwa mata zaman jego - Haihuwa na biyu ne 'yar uwarta ta je zama da ita, saboda mahaifiyarta ta rasu tuni - Cikin wata daya mijinta ya dirka wa 'yar uwar ciki kuma ya aureta duk da bata so ba Wata matar aure ta wallafa labarinta mai cike da taba zuciya. 



Ta bada labarain yadda 'yar uwarta makusanciya ta koma kishiyarta dare daya. A kokarinta na bai wa wata kwarin guiwar shawo kan matsalar aurenta, ta bada labarin yadda ta yi haihuwa ta biyu amma saboda rashin uwa, sai 'yar uwarta ta je mata zaman jego. 


Kamar yadda ta bayyana, bayan isowar 'yar uwarta, sai ta fara wata boyayyar alaka da mijinta. Babu dadewa kuwa 'yar uwarta ta samu juna biyu kuma mijin ta ne ya dirka mata, The Nation ta wallafa. 


Cike da alhini tare da tashin hankali ta dinga rokon 'yar uwarta da ta bar mata mijinta, amma 'yar uwar ta ce bata san wannan ba. Babu jimawa mijinta ya sanar da ita shirinsa na auren 'yar uwarta, wanda hakan ta faru. 



Mahaifiyar yara hudu ta ce a halin yanzu tana da 'ya'ya hudu yayin da 'yar uwarta da ta aure mijinta ke da 'ya'ya uku.


Source: Legit 


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "'Yar uwata da ta zo min zaman jego ta yi wuff da mijina, Matar aure "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?