--
Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki bidiyon daliban Kankara da suka sace Kalli Bidiyon Anan

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki bidiyon daliban Kankara da suka sace Kalli Bidiyon Anan

Don karyata jawabin gwamnan Katsina, Boko Haram ta saki bidiyin yaran da ta sace - A ranar Laraba Masari ya ce Abubakar Shekau makaryaci ne, ba shi ya sace daliban ba Daya daga cikin yaran ya yi gajeren jawabi cikin faifan bidiyon,



Shugaban yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki bidiyon tabbatarwa gwamnatin tarayya cewa shi da yaransa suka sace daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara, jihar Katsina ranar Juma'a. 


HumAngle ta samu faifain bidiyon wanda ya tabbatar da cewa daliban na raye kuma yan ta'addan na shirin tattaunawa da gwamnati. An saki bidiyon mai tsawon minti shida da sakwan 30 inda daya daga cikin yan ta'addan yayi jawabi kuma aka nuna hoton daya daga cikin daliban. 


Hakazalika ana iya ganin sauran daliban a bayansa sun yi datti kuma da alamu suna cikin daji. Daya daga cikin daliban wanda yayi magana a Turanci da Hausa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tattauna da yan ta'addan kuma ya bada shawaran kada ayi amfani da karfin bindiga. 


A cikin bidiyon ana iya sauraron dalibin yana cewa: "Ku taimaka, wajibi ne ka rusa dukkan yan sa kai, ka kulle dukkan makarantu, amma banda Islamiyya." "Ku mayar da dukkan Sojojin da kuka turo." Hakazalika ana iya sauraron daya daga cikin yan ta'addan yana yiwa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, martani kan karyata Shekau da yayi.


Kalli bidiyon: 



 SOURCE: LEGIT.NG


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun saki bidiyon daliban Kankara da suka sace Kalli Bidiyon Anan"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?