Yanzu yanzu: Buhari ya bada umurnin bude iyakokin kasa guda huɗu
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a bude iyakoki guda hudu - Shugaban kasar kuma ya ce a bude sauran iyakokin kasar zuwa karshen shekara Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin bude iyakokin kasa guda hudu ba tare da bata lokaci ba kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.
A umurnin da ya bada a ranar Laraba, shugaban kasar ya kuma bada umurnin bude sauran iyakokin kasar zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2020.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin bude wasu iyakokin kan tudu guda hudu
Ministar Kudi ce ta sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron FEC:
Labari da dumi-duminsa da Jaridar Legit.ng Hausa ta samu daga shafin gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu.
A cikin takaitaccen kanun labarai da Channels ta wallafa, ta bayyana cewa umarnin bude iyakokin zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamba, 2020.
Iyakokin guda hudu da za'a bude sune kamar haka: Illela a Jihar Sokoto, Maigatari a jihar Jigawa, dukkansu a arewacin Nigeria. Sai kuma iyakar Seme da ke Jihar Legas, yankin kudu maso yamma, da iyakar Mfun da ke yankin kudu maso kudu.
Daily Nigerian ta rawaito cewa ministar kudi, Zainab Ahmed, ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin ganawarta da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Sanarwar bude iyakokin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar NSMC ta kwatanta rashin tsaron Najeriya da rashin tsaron iyakoki, inda ta bayyana cewa hakan ne dalilin da yasa aka gaza cin nasara akan 'yaki da 'yan bindiga da Boko Haram.
Ta ce matsawar gwamnatin tarayya tana son cin nasara a kan rashin tsaro ta wuraren tafkin Chadi, wajibi ne a kula kwarai, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
Wadannan kadan ne daga cikin hanyoyin da za a tsare 'yan Najeriya daga cutarwar 'yan bindiga, kamar yadda mambobin kwamitin suka tattauna don samar da tsaro a kasar nan.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Yanzu yanzu: Buhari ya bada umurnin bude iyakokin kasa guda huɗu "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?