--
'Yan ta'adda sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda, an tsinci gawarsa gefen hanya

'Yan ta'adda sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda, an tsinci gawarsa gefen hanya


Wasu 'yan ta'adda da ake zargin cewa 'yan fashi da makami ne sun hallaka mataimakin kwamsihinan 'yan sanda, Egbe Edum - Edum, mai mukamin kwamishinan 'yan sanda, ya gamu da ajalinsa a hanyarsa ta zuwa gida domin ganin iyalinsa 


'Yan ta'adda sun kai farmaki kan Edum yayin da ya ke tafiya a gefen wata babbar hanya bayan motarsa ta lalace da tsakar dare Wasu miyagun 'yan ta'adda, da har ya zuwa yanzu ba'a tantance su waye ba, sun kashe babban jami'in dan sanda a yankin kudu maso kudu. 


Dan sandan, Egbe Edum, mai mukamin mataimakin kwamishinan 'yan sanda, ya gamu da ajalinsa a kan hanyarsa ta zuwa ganin iyalinsa a jihar Kuros Riba. 'Yan ta'addar sun kai wa Edum hari da safiyar ranar Laraba a yankin garin Calabar, babban birnin jihar Kuros Ribas.


Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ta tabbatarwa da jaridar Premium Times faruwar lamarin. "Duk da har yanzu mu na kan gudanar da bincike, takaitaccen bayanin da ke hannunmu ya nuna cewa ya zo gari ne daga Maiduguri domin ziyarar iyalinsa. Shi dan asalin nan ne.


"Ya iso nan da misalin karfe 1:00 na dare, amma sai motarsa ta samu matsala a kan hanya, har ma ya Kira matarsa domin ta zo ta dauke shi. "Ya na cikin tafiya da kafa a gefen hanya ne sai wasu miyagun batagari su ka far masa da sara da suka," a cewar Ugbo. 


Kakakin ta bayyana cewa ana zargin 'yan fashi ne suka kai wa Edum hari. Wata jaridar jihar Kuros Riba da ke wallafa labaranta a yanar gizo, CrossRiverWatch, ta wallafa labarin dauke da hoton motar Edum kaca-kaca da jini a gefen wata babbar hanya da ke Calabar. Takardun motar sun tabbatar da cewa marigayi Edum ne ya mallake ta. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "'Yan ta'adda sun kashe mataimakin kwamishinan 'yan sanda, an tsinci gawarsa gefen hanya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?