'Yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai a makarantar sakandire a Katsina
Labarin da duminsa na nuni da cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai daga dakinsu na kwana a makarantar Sakandiren Kankara - Ya zuwa yanzu ba'a san adadin daliban da 'yan bindigar suka tafi da su daga makarantar ba
Ana suraron fitowar jawabin rundunar 'yan sanda ko wata hukumar tsaro daga jihar Katsina Labari da dumi-duminsa da Legit.ng Hausa ta samu jaridar HumAngle ya bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai daga wata makarantar sakandire ta kimiyya da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.
A cewar HumAngle, 'yan bindigar sun shiga har dakin kwanan daliban tare da yin awon gaba da su da duku-dukun safiyar yau, Asabar. HumAngle ta wallafa cewa ana kidayar adadin daliban da aka sace a yayin da ta wallafa labarin da dumi-dumi a shafinta na sada zumunta; tuwita.
"Da duminsa: 'Yan bindiga sun dira makarantar sakandiren kimiyya da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, arewa maso yammacin Nigeria, tare da yin awon gaba da dumbin dalibai daga dakinsu na kwana da sanyin safiyar yau. Ana cigaba da kidayar adadin daliban da 'ya bindigar suka sace," kamar yadda HumAngle ta wallafa a tuwita.
Breaking: Dozens Of Secondary School Students Kidnapped In Katsinahttps://t.co/kBXBin9S4g
— HumAngle_ (@HumAngle_) December 12, 2020
Jihar Katsina na daga ckin jihohin arewa maso yammacin Nigeria da ke fama da matsalar 'yan bindiga. 'Yan bindiga na cigaba da kai hare-hare a sassan jihar duk da yawan jamu'an tsaro da aka tura da kuma atisaye daban-daban da suka kaddamar a yankin.
A baya, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya taba yin sulhu da 'yan bindiga domin a samu zaman lafiya.
Sai dai, sulhun bai yi wani tasiri ba, saboda 'yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare tare da kisan mutane babu gaira, babu dalili, tare da yin awon gaba da dukiyoyinsu. Bayan asarar rayuka da dukiyoyin al'umma, 'yan bindiga na sace mutane tare da yin garkuwa da su domi neman kudin fansa.
Wanna shine karo na farko da rahoto ya bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga makarantar kwana tare da yin awon gaba da dumbin dalibai a jihar Katsina.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "'Yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai a makarantar sakandire a Katsina "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?