Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta ɗage zamanta da kungiyar ASUU
Har yanzu takaddama ta ki karewa a tsakanin kungiyar malaman jami'o'i da gwamnatin tarayya - Gwamnatin tarayyya ta yi ikirarin cewa ta biya dukkan bukatun kungiyar ASUU
A nata bangaren, ASUU ta kafe a kan cewa ba za ta janye yajin aiki ba sai an biya mambobinta dukkan albashinsu da aka rike Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta ɗage zaman sulhuntawa tsakanin ta da ƙungiyar malaman jami'o'i ta ASUU.
Ɗage taron ya zo ne cikin wani saƙo da Mr. Charles Akpan, mataimakin babban daraktan ma'aikatar ƙwadago da ayyuka, ya fitar.
A cewar saƙon, "an ɗage Zaman sulhuntawa tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya wanda aka sanar za'a yi shi yau Laraba da misalin ƙarfe 3 na rana, muna gode muku abisa fahimtarmu."
Ƙungiyar ASUU ta shiga yajin aiki tun watan Mayun wannan shekarar sakamakon ƙin biyan haƙƙoƙinsu da sakin kuɗaɗen gyare gyare da batun shiga sabon tsarin biyan albishi na IPPIS da sauransu.
A baya bayan nan, Ministan ƙwadago da Ayyuka, Sanata Chris Ngige, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya ta yarda ta biya Naira biliyan ₦70 a matsayin haƙƙoƙin malaman da kuɗaɗen wasu jami'o'i guda uku sai kuma kuɗin gyare gyaren makarantu.
Ministan a ranar Laraba ya ce gwamnatin tarayya ta cika alƙawuranta da malaman jami'o'i, inda suka ce sun cika dukkan ƙa'idojin tayin da ƙungiyar ta gabatar.
"Alal misali, gwamnatin tarayya tayi alƙawarin kafa kwamitin sulhunta yarjejeniyar shekarar 2009 tun zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Marigayi Umaru Musa Ƴar'adua kuma sun cika alƙawarinsu na ƙaddamar da kwamitin inda Farfesa Munzali ke jagorantarsa."
"Ana nan ana bin hanyar da za'a biya Malaman haƙƙoƙinsu Naira biliyan ₦40, sai kuɗin farfaɗo da jami'o'i Naira biliyan ₦30, wanda ya kai adadin zuwa biliyan ₦70."
"Haka kuma tawagar ta kai ziyara jami'o'i wadda aka sahale ba za ta samu damar aiwatar da ayyukanta ba har sai an buɗe jami'o'in da aka rufe."
"Hakazalika, gwamnati ta amince zata biya haƙƙoƙin malamai ta wata kafar zamani da ba ta kai ingancin IPPIS ɗari bisa ɗari ba, kafin a kammala gwajin ingancin tsarin UTAS wanda ASUU ta kawo, a hukumar Cigaban fasaha ta ƙasa (NITDA)."
"Saboda haka ina mai bayyana cewa mun cika ƙa'idojin duk tayin da muka alƙawarta a ɓangaren gwamnati," a cewarsa. A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta yi martani game da kalaman shugaban kungiyar ASUU na cewa tayi alkawarin biyan dukkan albashinsu kafin su janye yajin aiki Ngige yace hasali ma sun cimma yarjejeniya a taronsu na karshe cewa ASUU zata janye yajin aiki ranar 9 ga watan Disamba.
Ya ce bayan janye yajin aikin ne ministocin ilmi da kwadago za su nemi a janye dokar 'Ba bu aiki, babu albashi' sannan a biya malaman sauran albashinsu.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta ɗage zamanta da kungiyar ASUU "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?