Wasu kananan yara ne rike da manyan bindigogi: Yaran da ya bayyana a bidiyon Shekau ya yi magana bayan kubuta
Daya daga cikin daliban makarantar gwamnatin GGSS Kankara, a jihar Katsina, ya yi bayani abubuwan da suka fuskanta cikin kwanaki shidan da suka yi hannun yan bindiga. Dalibin, wanda yayi ikirarin cewa shi ya bayyana a bidiyon da Boko Haram ta saki ranar Alhamis, ya ce yan bindigan ne suka fada masa abubuwan da ya furta bidiyon.
"Su suka ce in fadi su yan Boko Haram ne - yan bangaren Abu Shekau," ya fadi. "Abinda na fahimta shine ba yan Boko Haram bane." Yaran wanda yayi magana da tashar Arise TV kuma Legit ta saurara ya kara da cewa, "maganar gaskiya, barayin sun firgita lokacin da suka ga jirage.
Su suka sani inyi magana a bibiyon don fadawa gwamnati su daina turo jirage, idan ba haka ba zasu kashemu." "Mun sha bakar wahala, suna dukanmu dare da rana. Sau daya suke bamu abinci a rana." "Wasu daga cikinsu yara ne kawai da manyan bindigogi."
Source: Legit
0 Response to "Wasu kananan yara ne rike da manyan bindigogi: Yaran da ya bayyana a bidiyon Shekau ya yi magana bayan kubuta"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?