--
Tsaro: An fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha a Kaduna

Tsaro: An fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta sanar da cewa ta fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha domin tabbatar da tsaro jihar 


Kwamishina kananan hukumomi a Kaduna, Ja'afaru Sani, ya ce tantance matasan shine mataki na farko wajen samar da 'yan sandan jihar 



Sanata Uba Sani ya ce ya na aiki a kan kudirin da zai bayar da damar samun 'yan sandan tarayya da na jihohi 


Gwamnatin Kaduna ta fara tantance matasa a kokarinta na shirin fara aiki da 'yan sandan jiha domin inganta tsaro a jihar, kamar yadda TheCable ta rawaito. 


Uba Sani, Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, shine ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani taro da ma su ruwa da tsaki a sha'anin tsaro. 


Hadiza Balarabe, mukaddashiyar gwamnan jihar Kaduna, ita ce ta jagoranci taron da aka yi a Kaduna. 


Taron ya samu halartar 'yan majalisar jiha da na tarraya daga Kaduna, shugabannin kananan hukumomi 15 da ke arewacin Kaduna, da hakimai. 


Da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron, Sanata Sani ya bayyana cewa ya na aiki a kan kudirin neman sake fasalin 'yan sanda domin fuskantar kalubalen tsaro da kasa ke fama da shi. 


A cewarsa, idan kudirin ya samu karbuwa a majalisa, za'a kirkiri 'yan sandan jiha. "Ina aiki a kan wani kudiri da zai sauya fasalin aiki da kunshin rundunar 'yan sanda, hakan zai bayar da damar samun 'yan sandan jiha da na tarayya. 


Mu na son kawo karshen kalubalen tsaro a jihar Kaduna da Nigeria baki daya. 


"Za mu yi aiki da jama'a wajen magance matsalar tsaro a jiha, ta hanyar aiki kafada da kafada da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin siyasa. 


Gwamnan jiharmu a shirye ya ke tsaf domin kawo karshen matsalar tsaro," a cewar Uba Sani. A nasa bangaren, kwamishinan kananan hukumomin jihar Kaduna, Ja'afaru Sani, ya ce tantance matasan shine mataki na farko wajen samar da 'yan sandan jiha.


 A cikin watan Mayu na shekarar 2019 ne babba sifeton rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya sanar da cewa shugaba Buhari ya bashi izinin fara tsara hanyoyin samar da 'yan sandan jiha a fadin Nigeria. 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Tsaro: An fara tantance matasan da za'a dauka 'yan sandan jiha a Kaduna "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?