Surukarki kishiryarki: Aisha Yesufu ta gargadi ma'aurata da faɗa wa iyaye mata sirrukan su
Mai fafutukar kare hakkin dan adam Aisha Yesufu ta ce duk ma’auratan da ke sanar da iyayensu mata abunda ke wakana a gidajensu toh ta kare masu A cewar Aisha, ya zama dole ma’aurata su koyi boyewa iyayensu mata sirrikan aurensu idan har suna so yayi karko
Yayinda wasu yan Najeriya suka yarda da shawarar matar, wasu sun nuna rashin amincewarsu Matar nan da ke fafutukar kare hakkin dan adam, Aisha Yesufu, ta je shafin soshiyal midiya domin shawartan ma’aurata a kan su dunga boyewa iyayensu mata sirrikan gidan aurensu idan har suna so yayi karko.
A cewar Aisha, akwai matsala idan har ma’aurata suka fara sanar da iyaye mata abunda ke gudana a gidajensu.
Ta wallafa cewa:
“Idan kayi aure, mutum na farko da ya kamata ka tabbatar da ka boye wa sirrin gidan aurenka itace MAHAIFIYAR KA! Wadannan nan soyayya da kulawar da son sanin ko komai na tafiya daidai duk da sunan soyayya? Akwai matsala! Kana fara sanar da ita abunda ke wakana toh ta kare maka! Sai su fara shiga sharo ba shanu! "
A matsayin sabbi aure, ku koyi abunda zai fisshe ku. Abu na daban ne. Ku gina shi da kanku yadda kuke so. Ku fitar da kowa daga cikinsa! Ku yi abunku kuma ba abu mai sauki bane kulla auren mutane biyu mabanbanta. Don haka ku dauki lokain ku. Ku fitar da kowa daga ciki kuyi son ranku."
As a new couple, learn what works for you. It is unique. Develop it yourself the way you want to. Keep everyone out of it! Do your thing and it is never easy marrying two different lives together. So take your time.
— Aisha Yesufu (@AishaYesufu) December 11, 2020
Keep everyone out and do you!
Mutane da dama sun je shashin yin sharhi domin sanar da ra’ayinsu yayinda wasu suka yarda da ita, wasu kuma sun nuna rashin amincewarsu. Wani mai amfani da Twitter @Egi_nupe_ ya rubuta: “A koda yaushe yana da matukar wahala domin iyaye mata na yin hakan ne saboda soyayyarsu ga yaransu.”
@koladechris ya rubuta: “Ka boyewa mahaifiyarka sirrin aurenka a kan wani dalili? Wannan kwata-kwata baya bisa turba. Shin Aisha Yesufu ta yi nasarar hana mahaifiyarta da sirikarta shiga lamuran aurenta?” @RilCeeJay ya yi martani da:
“Kada ki yi fushi yaruwa amma b azan taba daukar aurena da muhimmanci fiye da mahaifiyata/iyayena ba. Bugu da kari ba zan taba auren yariyar da mahaifiyata bata yi na’am da ita ba. Ba zan taba zama tushen bacin ran mahaifiyar da ta kawoni duniyarnan ba saboda na samu abar so. Sam, ba dani ba!”
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Surukarki kishiryarki: Aisha Yesufu ta gargadi ma'aurata da faɗa wa iyaye mata sirrukan su "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?