
Siyasar Kano: APC ta sauke shugabannin jam'iyyar ma su biyayya ga Ganduje
Hssaini Mairiga, shugaban tsagin jam'iyyar APC a jihar Kano, ya sanar da sauke daya tsagin da ke karkashin jagorancin Abdullahi Abbas
Mairiga ya ce Abbas da sauran mukarrabana sun samu shugabanci ne ta barauniyar hanya - Kazalika, ya gargadi ma su burin shiga takarar zaben kananan hukumomi su guji siyen fom din takara daga wurin shugabancin Abbas
Wani tsagin jam'iyyar APC a jihar Kano, a karkashin jagorancin Hussaini Isa Mairiga, ya sanar da sauke shugabannin tsagin jam'iyyar a karkashin jagorancin Abdullahi Abbas, kamar yadda Thecable ta rawaito.
An sake zaben shugabannin tsagin jam'iyyar APC da ke karkashin jagorancin Abbas a shekarar 2018 saboda rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar a shekarar 2017. Tsagin da Abbas ya ke jagoranta shine mai daurin gindin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje.
Da ya ke magana da manema labarai a ranar Alhamis, Mairiga ya ce Abbas da sauran mukarabbansa sun karbi shugabancin APC ne ta barauniyar hanya, ta hanyar zaben da ya raba kan mambobin jam'iyya.
"Ta hanyar zaben bogi Abdullahi Abbas ya zama shugaban jam'iyya, amma duk da hakan, ya gaza tabuka komai bayan mulkin kama karya.
"Ba halastattun shugabanni bane, shugabancinsu ya sabawa kundin tsarin mulkin jam'iyya, a saboda haka duk wani abu da ya fito ta karkashinsu haramtacce ne. "Abinda na ke nufi a nan shine; duk wani dan takarar a zaben kananan hukumomi da za'a yi a watan Janairu kar ya sayi fom din takara ta hannun haramtattun shugabanni.
"Duk Wanda ya shiga takara ta hannunsu ya shiga asara don ko ya ci zabe sai an kwace a kotu," a cewarsa. A karshe Mairiga ya bukaci shugabancin APC na kasa ya kafa kwamitin riko na jam'iyyar a jihar Kano domin ya gudanar da sabon zaben shugabanni na gaskiya.
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Siyasar Kano: APC ta sauke shugabannin jam'iyyar ma su biyayya ga Ganduje "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?