
Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, ya caccaki shugaban rundunar sojin kasa a kan wasu kalaman da ya furta
Ya yi wannan caccakar ne a shafinsa na Twitter, a ranar Alhamis, inda yace basirar Buratai ta kare alamu ne na yana bukatar murabus
Buratai ya ce ta'addanci zai iya cigaba da wanzuwa har nan da shekaru 20 masu zuwa, wadannan ne suka fusata sanatan Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a ranar Alhamis, ya caccaki shugaban rundunar sojin kasa, Lt. Janar Tukur Buratai, a kan yadda yace ta'addanci zai iya cigaba da wanzuwa har nan da shekaru 20 a Najeriya.
The Punch ta ruwaito yadda shugaban sojin kasa yayi wata magana bayan 'yan kwanaki da 'yan Boko Haram suka kashe manoman shinkafa 43 a jihar Borno.
Tsohon sanatan ya mayar da martani a kan maganar, ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter a ranar Alhamis, inda yace kalaman Buratai suna nuna karewar basira da rashin dabarun yaki.
Kamar yadda Shehu Sani ya wallafa, "Sanar da mutanenmu cewa tabarbarewar harkokin tsaro za su cigaba har na tsawon shekaru 20 alamace da ke nuna gazawa da karewar basirarka a matsayinka na soja.
"Kuma alama ce wacce take nuna kana bukatar murabus, sannan kuma kana nuna wa duniya alamar cire rai daga samun nasara ne."
SOURCE: LEGIT
0 Response to "Shehu Sani ya yi wa Buratai 'wankin babban bargo' a kan wa'adin da ya bai wa Boko Haram "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?