--
Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa

Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa


Majalisar dattawa ta mika bukatu bakwai ga shugaba Buhari na shawo kan lamarin tsaro - Na farko ciki shine ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya 


Sanata Babba Kaita ya yi alhinin rashin amfanin makudan kudaden da ake baiwa Sojoji kowace shekara Sanata mai wakiltan Katsina ta Arewa, Ahmad Babba-Kaita, ya yi Alla-wadai da hare-haren da ake kaiwa sassan kasar nan. 


Yayin jawabi a zauren majalisa ranar Talata, Kaita ya ce abubuwan da gwamnatin nan ke yi basu haifar da 'da mai ido ba har yanzu. Ya ce idan ba'a dau mataki ba, yan bindiga zasu kwace kasar. Dan majalisan wanda ke wakiltan mazabar Buhari a majalisar dattawa, ya ce wajibi ne a binciki shugabannin Sojoji kan makudan kudaden da ake basu domin yakar ta'addanci. 


"Lokacin fadin gaskiya yayi. Ba bu dan Najeriyan da zai cigaba da yarda da abinda ke faruwa. Ba zai yiwu mu cigaba da jimamin mutuwar mutane ba kullum, " yace. "Ba zamu amince da bayanan wadanda ya kamata suyi abinda ya dace ba duk lokacin da aka kai hari. Idan da gaske Garba Shehu ya fadi haka, to gaskiya akwai rashin tunani." 


"Ta yaya za'a kashe mutanen da suka je gonakinsu noma duk da talaucin da ake ciki kuma su rasa rayukansu amma wani yace basu nemi izini ba. Ba'a girban kayan gona a rana daya, muna girba na tsawon lokaci." 


SOURCE: LEGIT


Mtn Data Bonanza By Bz Global Services 🌐

1GB @N350 

2GB @N700

3GB @N1,050

4GB @N1,400

5GB @N1,750

Validity For 30Days

Hanyar Biya Bank Transfer Domin Siya Yanzu Kiramu Ta Number Waya 08133888333 Koka Aiko Sako Ta Whatsapp: 09066633320


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Sanatan da ke wakiltar Daura, Ahmad Babba-Kaita, ya caccaki fadar shugaban kasa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?